Muhammad Malumfashi
20368 articles published since 15 Yun 2016
20368 articles published since 15 Yun 2016
Rahotanni daga kasar Mexico sun nuna cewabsanatoci su ba hammata iska a zaman ranar Laraba, inda lamarin ya kai ga doke doke da ture-ture a zauren Majalisa.
Dakarun sojojin Najeriya sun yi wani kazamin artabu da 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sojojin sun samu nasarar fatattakar miyagun tare da kwato babura.
A labarin nan, za a ji cewa kuniyar kwadago ta kasa, NLC ta bayyana jin dadin yadda gwamna Uba Sani ya fara gyara kuskuren Nasir El-Rufa’i a Kaduna.
A jihar Bauchi, dan sanda ya harbe soja yayin takaddama kan wata motar da ake zargin tana dauke da ma’adanan da aka hako ba bisa ka'ida ba a garin Futuk.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar gani da ido zuwa kauyen Gidan Mantau, inda miyagun 'yan bindiga suka kashe masallata masu yawa.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Tukur Kola ya rasu bayan fama da rashin lafiya mai tsawo. Shi ne shugaban Izala na Birnin Kebbi a jihar Kebbi kafin rasuwar shi.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar Arewa Consultatibe Forum ta nemi gwamnatin tarayya da ta jihar Legas da su bayar da diyya ga mutanen kasuwar Alaba Rago.
'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun shiga wasu kauyuka a jihar Zamfara sun sace mutum 100 a wani hari da suka kai. Mutanen sun ce sun zamo bayi a kasarsu.
Gwamnatin tarayta ta kaddamar da shirin karfafa mata a fannonin noma da kiwo a Najeriya, za a taimakawa mata akalla miliyan 10 a fadin jihohin Najeriya.
Muhammad Malumfashi
Samu kari