Muhammad Malumfashi
20368 articles published since 15 Yun 2016
20368 articles published since 15 Yun 2016
Gwamnatin jihar Neja ta kafa dokar hana wa'azi ba tare da lasisi ba. Ana bukatar kowane malami ya nemi izini daga hukumar kula da addini kafin cikar wata biyu.
'Yan sanda sun gayyaci tsohon Gwamna Nasir El-Rufai da wasu kusoshin ADC 6 domin amsa tambayoyi kan zargin hada baki da tayar da zaune tsaye a jihar Kaduna.
Sabuwar annobar cutar Ebola da ta bulla a DR Congo ta kashe mutane 15, WHO ta ce tana aiki cikin gaggawa tare da amfani da rigakafin Ervebo domin dakile cutar.
Rundunar ‘yan sanda a Kano ta gayyaci shugabar karamar hukumar Tudun Wada a jihar, Sa’adatu Salisu kan zargin umartar harbe wasu ma'aikatan kamfani.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da sace basaraken gargajiya na Bagaji Odo, David Wada, yayin da yake dawowa daga wani taron sarakuna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jagoran yan ta'adda, Kachalla Abu Dan Barka, da wasu mayaƙansa huɗu sun mutu a harin abokan gaba a karamar hukumar Maru, Zamfara.
Matasan karamar hukumar Shagari da ke jihar Sakkwato sun bukaci gwamnati ta dauki matakan dawo da zaman lafiya ko kuma su dauki matakin kare kansu.
Gwamnonin Arewa maso Gabas sun mika jerin bukatunsu na tsaro da ababen more rayuwa ga shugaba Tinubu don tallafawa ci gaban yankin. Tinubu ya kwantar da hankulansu.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna matukar bacin ransa bayan 'yan sanda sun kawo cikas ga shirin shugabannin ASC na gudanar da taro.
Muhammad Malumfashi
Samu kari