Muhammad Malumfashi
20368 articles published since 15 Yun 2016
20368 articles published since 15 Yun 2016
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa akwai hannun Shugaban kasa Bola Tinubu da APC wajen kunno rikici a jam'iyyun adawa.
Wata dattijuwa mai suna Victoria ta ce yan sanda sun hallaka danta mai suna Moses da ya je gidan gwamna don isar da saƙon Ubangiji da yi masa wa'azi.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya taya Sarki Muhammadu Sanusi II murnar gama digirin PhD a jami'ar London. Jami'ar za ta yi hadaka da jami'ar North West ta Kano.
Gwamnan jihar Benuwai ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta kula da mata da yayan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren yan bindiga.
Rundunar yan sanda ta cafke wasu mutane guda hudu a jihar Sokoto da ake zargin sun farmaki mataimakin gwamnan jihar da ke dawowa daga ziyarar jaje.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa a shirye yake don ganin an kawar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
A shekarar 2026 sabon harajin shugaba Bola Tinubu na 5% zai fara aiki a Najeriya. Harajin zai shafi 'yan kasuwa, ma'aikata, malamai dalibai da duk 'yan Najeriya.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya jagoranci sallar Juma'a a wani masallaci da kwamishinan ilimin jihar Dr. John D.W. Mamman da Kirista ne ya gina.
Al'ummomin wasu yankuna a jihohin Imo da Anambra sun koka cewa yan bindiga na tilasta musu biyan kuɗin haraji kafin su birne mamatansu da suka rasa.
Muhammad Malumfashi
Samu kari