Muhammad Malumfashi
21427 articles published since 15 Yun 2016
21427 articles published since 15 Yun 2016
Yan majalisar Amurka biyu, Gregory Meeks da Sara Jacobs, sun soki barazanar Trump ta daukar matakin soja kan Najeriya, suna kiranta rashin hankali da ganganci.
Kashim Shettima ya tafi Brazil don wakiltar Tinubu a taron COP 30, inda zai gabatar da jawabi kan yanayi, makamashi, da kasuwar carbon domin ci gaban Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya mika sunan Kingsley Tochukwu Udeh, SAN, wanda yake babban lauyan Enugu, domin majalisar dattawa ta tabbatar da shi a matsayin minista.
Tinubu ya nemi majalisar tarayya ta amince ya karbo sabon bashin ₦1.15trn don rage gibin kasafin kuɗi, mako guda bayan amincewa da bashin waje na $2.847bn.
Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Dick Cheney, ɗaya daga cikin manyan masu fadi a ji a tarihin siyasar kasar, ya rasu yana da shekaru 84 bayan fama da ciwon zuciya.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi kalamai masu kaushi kan shugaban jam'iyyar PDP na kasa. Ya ce bai da hali mai kyau na jagoranci.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Edo sun samu nasarar cafke wata matar aure da ta shirya shirin yin garkuwa da ita don karbar kudade a hannun mijinta.
Babbar kotun jihar Oyo mai zama a Ibadan ta umarci shugaban jam'iyyar PDP na lasa, Ambasada Umar Damagum ya ci gaba da shirin taron PDP kamar yadda aka tsara.
Kotu a Ilorin ta wanke mata biyu da ake zargi da mallakar bindiga, yayin da ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga 'yan fashi da makami uku a Kwara.
Muhammad Malumfashi
Samu kari