Muhammad Malumfashi
21424 articles published since 15 Yun 2016
21424 articles published since 15 Yun 2016
Wasu makiyaya sun koka game da harin da aka kai musu a wasu yankunan jihar Benue. Sun ce an kashe musu shanu 259 jerin hare haren da aka kai musu a Benue.
Wasu daga cikin matan da aka sace a GGSS Maga a jihar Kebbi sun kubuta. Mata biyu ne suka kubuta yayin da 'yan bindiga ke tafiya da su cikin daji.
Gagarumar sauya sheƙa ta auku a Taraba yayin da shugaban PDP, kwamishinoni, ‘yan majalisa da shugabannin kananan hukumomi suka bar PDP suka koma APC.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da ya ziyarci Kebbi domin jajantawa da kuma tabbatar da ceto ɗaliban da aka yi garkuwa da su.
Umar Sani ya bayyana cewa Nyesom Wike ya bukaci PDP ta janye takarar shugaban kasa a 2027, ko kuma ta fuskanci rikici mai tsanani cikin jam’iyyar gabanin zaben.
Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya dakatar da shirin shiga jam'iyyar APC sakamakon sace dalibai mata a jihar Kebbi. Ya yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta ceto yaran.
'Yan bindiga sun sako wasu daga cikin mutanen da suka sace a jihar Katsina. An sako mutanen ne a shirin sulhu da ake yi da 'yan bindigan domin samun zaman lafiya.
A labarin nan, za a ji cewa wasu da ba a kai ga gano su ba sun yi kutse a cikin wayoyin Alhaji Aliko Dangote da Femi Otedola a cikin mako gida, inda aka nemi kudi.
Gwamnatin Katsina ta umarci Malam Yahaya Masussuka ya kare kansa gaban malamai. Ana zargin karatuttukan malami sun sabawa koyarwar addinin Musulunci.
Muhammad Malumfashi
Samu kari