Muhammad Malumfashi
21376 articles published since 15 Yun 2016
21376 articles published since 15 Yun 2016
Hukumar IEA ta bayyana cewa ci gaba da yakin Iran, Amurka da Isra'ila zai jawo gagarumar matsala ga makamashi a fadin duniya yayin da ake ci gaba da gwabza yaki.
Jirgin saman kasar Canada ya yi hadari yayin sauka a wani filin jirgin jiragen sama a birnin New York na kasar Amurka. An rufe filin jirgin zuwa wani lokaci.
Amurka ta fito fili ta fadawa Isra'ila cewa yaki da Iran zai dauki lokaci mai tsawo kafin a kawo karshensa. Wani rahoto ya ce yakin zai iya kaiwa Satumban 2026.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya hado Peter Obi na jam'iyyar ADC, Seyi Makinde na PDP da wasu 'yan adawa a jihar Kano yayin da ake shirye-shiryen 2027 a siyasar Najeriya.
Shugaban Iran ya bukaci ƙungiyar BRICS ta taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, ya zargi Amurka da Isra’ila kan hare-haren da suka kai.
A labarin nan za a ji cewa wani masanin halayyar masu aikata laifuffuka, Dr. Sulaiman Ishaq Muhammad ya shawarci gwamnati game da ƴan ta'adda a soshiyal midiya.
A labarin nan, za a ji cewa kasar Iran ta bayyana dalilan da suka jawo takasa hakuri, har takai hari waɗansu sansanonin soji a Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna yiwuwar tsayawa takarar Sanata ta Arewa a 2027, bisa ga bukatun shugabanni da masu ruwa da tsaki.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya yi alhinin rasuwar hadiminsa, wanda ke tsare masa duk wasu ayyukan da zai yi, an ce ya rasu ne a wurin taro.
Muhammad Malumfashi
Samu kari