Ibrahim Yusuf
4245 articles published since 03 Afi 2024
4245 articles published since 03 Afi 2024
Kamfain sadarwa na MTN zai katse sabis a wasu yankuna na Kano, Adamawa da Borno na wasu lokuta a ranar Asabar, 25 ga Oktoban 2025 domin yin wani gyara.
Gwamnatin Kamaru ta sanar da cewa za ta gurfanar da matasa akalla 20 da aka kama a kotun soja kan zanga zangar bayan zaben shugaban kasa saboda tayar da tarzoma.
Jagoran jam'iyyar NNPP, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya yi gargadi kan neman dawo da zaben 2027 zuwa 2026. Ya ce lamarin zai kawo matsaloli da dama a Najeriya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Rabi Kwankwaso yayin murnar cikarsa shekara 69 da haihuwa. Ya ce Kwankwasiyya na nan daram a Kano.
Malamin addinin Musulunci a kasar Habasha, Mufti Haji Umer Idris ya rasu yana da shekara 90 a duniya. Sheikh Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwarsa.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ba wata budurwa, Joy Ogah damar zama mataimakiyar shugaban kasa na rana daya. Ta yi magana kan ilimin mata.
Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Borno na bincike kan wata budurwa ta kashe kanta saboda cewa an tilasta mata ta auri abokin babanta kuma bata so.
Ayatollah Ali Khamenei ya yi watsi da tayin zama da shugaban Amurka, Donald Trump ya masa kan mallakar nukiliya. Ya ce Amurka 'yar ta'adda ce kan rikicin Gaza.
Gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar tarayyar Turai za su samar da guraben ayyuka 20,000 a Najeriya. Za a samar da ayyukan ne karkashin shirin NJFP 2.0.
Ibrahim Yusuf
Samu kari