Ibrahim Yusuf
5413 articles published since 03 Afi 2024
5413 articles published since 03 Afi 2024
Mutane da kungiyoyi sama da 50 ne suka taru a birnin London domin adawa da shugaban Amurka, Donald Trump da ya ziyarci Birtaniya. Suna adawa da kai hari Gaza.
Dakarun rundunar sojin Najeriya ta kai samame wata masana'antar da ake hada makamai a jihar Filato. An kama bindigogi kiran gida da bindoga kirar pistol.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa yan kasuwa da ke shigo da man fetur daga kasashen waje sun nemi ya saka musu tallafin man fetur na Naira tiriliyan 1.5.
Kasar Saudiyya ta kulla yarjejeniyar tsaro da Pakistan mai makaman nukiya bayan yawan hare haren Isra'ila a Gabas ta Tsakiya. Kasashen za su kare juna.
Kasashen Afrika 4 ba su nuna goyon baya ga Gaza ko Isra'ila ba da aka kada kuri'a a majalisar dinkin duniya, Kamaru, Kongo, Sudan ta Kudu da Habasha na cikinsu.
Sanata Barau Jibrin ya karbi matasan NNPP da Kwankwasiyya da suka fito daga Danbatta zuwa jam'iyyar APC a Abuja. Barau ya ce NNPP ta kusa rushewa a Najeriya
Shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC ta Buhari na jihohi sun gana da Atiku Abubakar domin shirin kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zaben shubana kasa na 2027.
Attajirin Afrika ya bayyana kalulabalen da ya fuskanta wajen kafa kamfanin siminti a jihar Benue inda mutanen yankin suka hana shi sai ya tafi jihar Kogi.
Wasu da ake zargi 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ne sun sace wani mutum a karamar hukumar Dukku sun kashe shi bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 5.
Ibrahim Yusuf
Samu kari