Gwamnatin Tinubu Ta Fayyace Gaskiya kan Jita Jitar Ƙara Kuɗin Wutar Lantarki

Gwamnatin Tinubu Ta Fayyace Gaskiya kan Jita Jitar Ƙara Kuɗin Wutar Lantarki

  • Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan shirin ƙara kuɗin wutar lantarki a faɗin Najeriya, kamar yadda ministan wutar lantarki ya bayyana
  • Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya yi wannan bayani ne bayan yaɗuwar rahotannin da ke nuna cewa ana shirin ƙara kuɗin wutar lantarki nan ba da jimawa ba
  • Gwamnatin ta jaddada cewa babu wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a halin yanzu, yayin da ake jiran ƙarin bayani kan batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan jita-jitar da ake yadawa kan shirin ƙara kuɗin wuta.

Gwamnatin ta jaddada cewa ba ta da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki a faɗin Najeriya, kamar yadda ministan wutar lantarki, Joseph Tegbe, ya bayyana.

Kara karanta wannan

An kai ɗan Najeriya kotu kan ikirarin mallaka da shirin cefanar da jirgin sojoji

An karyata maganar shirin ƙarin kudin wuta a Najeriya
Sandunan wutar lantarki da ministan makamashi a Najeriya, Joseph Tegbe. Hoto: Ministry of Power.
Source: UGC

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bayar da wannan tabbaci ne yayin bikin aza harsashin ginin wasu ƙananan tashoshin samar da wutar lantarki guda biyar, cewar Channels TV.

Wurin da gwamnati ta fi mayar da hankali

Tashoshin na da alaƙa da juna, waɗanda za su samar da megawatt 17.7, tare da tsarin adana wutar lantarki mai ƙarfin megawatt-hour 17.74.

Ya ce gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar, yana mai tabbatar wa ’yan Najeriya cewa babu wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki.

Ya ce:

“Ina son bayyana wannan a sarari ba tare da wata ruɗani ba: babu wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki.
Abin da muke shirin yi shi ne samar da tsarin wutar lantarki da zai yi aiki dare da rana. Ƙudurarmu ita ce samar da wutar lantarki na sa’o’i 24 a kowace rana.”

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Tinubu ba zai iya zuwa kamfe a wasu jihohin Najeriya ba

Babu maganar kara kudin wutar lantarki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Getty Images

Shawarar minista makamash ga yan kasa

Ana gudanar da ayyukan ne a Bola, Jiboye, Molade-Adelubi, Ogo Oluwa da Sooko-Elega, kuma ana sa ran za su amfani al’ummomin da ke ƙananan hukumomin Akinyele, Ido, Ibadan ta Arewa, Egbeda da Lagelu a Oyo.

Ministan ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi watsi da bayanan da ba su da tushe game da yiwuwar ƙara kuɗin wutar lantarki, yana mai bayyana cewa babban abin da gwamnatin Tinubu ke ba muhimmanci shi ne tabbatar da samun ingantacciyar wutar lantarki a ƙasar.

Wannan bayani ya zo ne bayan yaɗuwar rahotannin da ke nuna cewa ana shirin ƙara kuɗin wutar lantarki nan ba da jimawa ba.

Za a daina dauke wuta a Najeriya

An ji cewa Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa kan samar da wutar lantarki ta awanni 24 a kowace rana a Kano da wasu biranen Najeriya.

Kara karanta wannan

Minista ya ɓallo ruwa a gaban ƙasashen duniya, ya yi maganar da ka iya juyo wa kan Tinubu

An ce gwamnatin ta fara wannan yunkuri ne a karkashin shirin Energy Zones, wanda zai shafi layin wuta na Lagos, Abuja-Kaduna-Kano da Enugu-Port Harcourt.

Gwamnatin ta ce wannan shiri zai fi mayar da hankali kan wuraren da bukatar wutar lantarki ta fi yawa domn tabbatar da ingantuwar wutar ko yaushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.