Kudi Sun Samu, An Raba Naira Tiriliyan 2.43 tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihohin Najeriya
- Kwamitin FAAC ya raba Naira tiriliyan 2.43 ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a matsayin kuɗaɗen shiga na watan Satumban 2026
- Gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 832.24, jihohi sun samu Naira biliyan 799.87, yayin da ƙananan hukumomi suka samu Naira biliyan 560.66
- Kuɗaɗen shiga sun ƙaru da Naira biliyan 246.38, daga Naira tiriliyan 2.85 a watan Agusta zuwa Naira tiriliyan 3.1 a Satumba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kwamitin Raba Kuɗaɗen Shiga na Tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.43 ga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi a watan Satumban 2026.
Hakan na cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis dauke da sa hannun Francis Kusa, babban jami’in yaɗa labarai kuma shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Kuɗi.

Source: Twitter
A rahoton da The Cable ta wallafa, ya ce an amince da rabon ne a taron FAAC na watan Oktoba, wanda Shamsudeen Ogunjimi, babban akawun tarayya, ya jagoranta.
FAAC ya raba kudaden shigar Satumba
Sanarwar ta bayyana cewa an samo kuɗaɗen ne daga jimillar kuɗaɗen shiga da suka kai Naira tiriliyan 3.91.
Daga cikin kuɗaɗen da aka raba, gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 832.24, yayin da jihohi suka samu Naira biliyan 799.87.
Ƙananan hukumomi kuma sun samu Naira biliyan 560.66, yayin da jihohin da ake hako man fetur suka karɓi Naira biliyan 236.05 a matsayin kaso kuɗaɗen shiga daga albarkatun ma’adinai.
A cewar sanarwar da aka fitar bayan taron, FAAC ya ware Naira biliyan 131.76 domin harkokin tattara kuɗaɗen shiga, yayin da aka ware Naira tiriliyan 1.35 don kuɗaɗen da za a tura, mayarwa da kuma ajiyewa.
Kuɗaɗen VAT sun ragu
FAAC ta ce kuɗaɗen shiga daga harajin kayayyaki da ayyuka (VAT) sun kai Naira biliyan 816.87 a watan Satumba, idan aka kwatanta da Naira biliyan 834.84 da aka samu a watan Agusta. Wannan na nufin an samu raguwar Naira biliyan 17.97.

Source: Getty Images
Sanarwar taron ta ce:
“Daga cikin kuɗaɗen, an ware Naira biliyan 23.576 domin harkokin tattara harajin, sannan aka ware Naira biliyan 36.709 da za a tura, mayarwa da ajiyewa.
“An raba ragowar Naira biliyan 756.587 tsakanin matakan gwamnati uku, inda gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 75.659, jihohi suka karɓi Naira biliyan 416.123, sannan ƙananan hukumomi suka samu Naira biliyan 264.805.”
IMF ya ba Najeriya shawara
Kun ji cewa asusun ba da limuni na duniya, IMF ya yi magana game da maganganu kan dawo da tallafin mai a Najeriya a halin yanzu
IMF ta ce tallafin man fetur yana kashe kuɗaɗen gwamnati sosai, yana fifita masu kuɗi, tare da ƙara matsin tattalin arziki da hauhawar farashi.
IMF ya gargadi Najeriya da kada ta dawo da tallafin man fetur ga kowa, inda ya ba da shawarar tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu radadin tsadar makamashi.
Asali: Legit.ng

