Ahmad Yusuf
11632 articles published since 01 Mar 2021
11632 articles published since 01 Mar 2021
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano, Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa, ya bayyana cewa a halin yanzun babu sarki ko ɗaya sai gwamna ya naɗa.
Kungiyoyin kwadago sun rage bukatarsu a mafi ƙarancin albashi amma sun ce ba za su karɓi sabon tayin da gwamnatin tarayya ta gabatar na N57,000 ba.
Rundunar ƴan sanda ta kubutar da yaran mamban majalisar dokokin jihar Zamfara waɗanda yan bindiga suka yi garkuwa da su watanni 17 da suka gabata.
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci ƴan kasuwar hada-hadar musayar kuɗi su sabunta lasisi kuma ya yi sababbin sauye-sauye ga lasisi mai daraja ta farko da ta 2.
Mamban majalisar dokokin jihar Kano ya ce da fushin sarakunan da Ganduje ya naɗa suka fara mulki kuma sun so rushe masarautun tun farkon rantsar da Abba Kabir.
Tsaren-tsaren CBN na ci gaba da ɗaga kimar kuɗin Najeriya yayin da Dalar Amurka ta kara karyewa a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata, 21 ga Mayu.
Sanata Garba Maidoki ya yi iƙirarin cewa a kowane wata Gwamna Nasiru Idiris na bai wa sojoji N500m domin su yi aikin tabbatar da tsaron al'umma a faɗin Kebbi.
Jami'an hukumar DSS da ƴan sanda sun kai ɗauki zauren majalisar dokokin jihar Kuros Ribas bayan ƴan majalisar sun tsige shugaba kan zargin almundahana.
Yan majalisar dokokin jihar Kano sun fara zaman yi wa dokar masarautun Kano garambawul, jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro don tabbatar da doka da oda.
Ahmad Yusuf
Samu kari