An Yi Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Alkalin Alkalai Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Babban Rashi a Najeriya, Tsohon Alkalin Alkalai Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon alkalin alkalai na jihar Benue, Mai shari'a Adam Onum ya rasu ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026 bayan fama da doguwar jinya
  • Shi ne mutum na farko dan kabilar Idoma da aka nada a matsayin Alkalin Alkalai na Jihar Benue tun kafuwar jihar a 1976
  • Gwamna Alia ya ce gudunmawar marigayin ga bangaren shari’a za ta ci gaba da kasancewa cikin tarihin jihar Benue

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue, Nigeria - Tsohon Alkalin Alkalai na Jihar Benue, Mai Shari'a Adam Onum, ya rasu bayan fama da doguwar jinya, lamarin da ya jawo alhini a bangaren shari’a da kuma tsakanin al’ummar jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa Onum ya rasu ne ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026. Marigayin ya kasance daya daga cikin fitattun jami’an shari’a da suka taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin shari’a a Jihar Benue.

Kara karanta wannan

Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC

Justice Adam Onum.
Tsohon alkalin alkalai na jihar Benue da ke Arewacin Najeriya, Mai shari'a Adam Onum Hoto: Piyadi Farms
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Adam Onum ya kafa tarihi a watan Disambar 2017, lokacin da aka nada shi a matsayin Alkalin Alkalai na Jihar Benue.

Nadinsa ya kasance wani muhimmin lamari ga al’ummar Idoma, domin shi ne mutum na farko dan kabilar da ya samu wannan mukami tun bayan kafuwar jihar a shekarar 1976.

Gwamna Alia ya yi alhini

Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon alkalin, inda ya ce gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa cibiyoyin shari’a da na bangaren alkalai za ta ci gaba da kasancewa cikin muhimman abubuwan tarihin Benue.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin sakon ta’aziyyar da babban sakataren yada labaransa, Tersoo Kula, ya fitar ranar Juma’a.

A sakon, Alia ya bayyana Onum a matsayin fitaccen lauya kuma jami’in shari’a wanda ya shafe shekaru yana gudanar da aikinsa cikin gaskiya, jarumtaka da jajircewa wajen tabbatar da adalci.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya ɗauko da zafi, ya kutsa wata jiha domin ba Tinubu ɗaruruwan ƙuri'u

Ya ce marigayin ya nuna wadannan halaye ne a tsawon shekarun da ya yi yana aiki a bangaren shari’a, inda ya sadaukar da kansa wajen gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa.

Gwamnan ya kara da cewa tarihin bangaren shari’a a Benue ba zai manta da ambaton rawar da Onum ya taka wajen bunkasa cibiyoyinta ba.

Sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin

Alia ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar Idoma, bangaren shari’a na Jihar Benue, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) da daukacin al’ummar jihar.

Ya ce rasuwar tsohon alkalin babban rashi ne ga wadanda suka san shi da kuma hukumomin da ya yi wa hidima.

Gwamna Alia.
Gwamnan jihar Benue, Hayacinth Alia yana hira da manema labarai a fadar gwamnatinsa da ke Makurdi Hoto: Rev. Hyacinth Lormem Alia
Source: Facebook

Gwamnan ya roki Allah Ya ba iyalan marigayin da bangaren shari’a karfin hali da juriyar wannan rashi mai radadi.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, tare da ba shi Aljannar Firdausi.

Shugaban FUT Minna na farko ya rasu

Kun ji cewa Farfesa Jonathan Ndagi, shugaban farko na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, babban birnin jihar Neja (FUT Minna), ya rasu.

Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sanar da rasuwarsa tare da jinjina wa gudummawar da ya bayar a fannin ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262