Ahmad Yusuf
11606 articles published since 01 Mar 2021
11606 articles published since 01 Mar 2021
Wasu tsagerun ƴan daba da suka saje da masu zanga zanga sun tafka ɓarna a hedkwatar jam'iyyar APC da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, sun lalata kayayyaki.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarwa ya bayyana cewa kowane lokaci daga yanzu gwamnatinsa za ta fara biyan ma'aikata sabon albashi mafi ƙaranci na N70,000.
Babbar kotun jihar Legas ta tsawaita umarnin taƙaita wuraren da ya halatta masu zanga-zangar yunwa sun je a faɗin jihar domin tabbatar da zaman lafiya.
Masu shirya zanga-zangar da ake yi a jihar Legas sun sanar da tafiya hutun kwana ɗaya tal domin duba abubuwaɓ da suka faru da ɗaukarmataki na gaba.
Gwamna Francis Nwifuru ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta rabawa matasa 1,300 tallafin kudi domim su dogara da kansu saboda ƙin shiga zanga zanga.
Jami'an tsaro sun damke masu ɗaukar nauyin telolin da ke dinka tutocin Rasha a Kano, hukumar DSS ta ce har yanzu tana kan bincike kan lamarin na cin amanar ƙasa
Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi tir da harin da wasu ƴan daba suka kai dakatariyarta da ke Gusau, babban birnin jihar, sun lalata muhimman kayayyaki.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda wani jami'in tsaro ya sa bindiga ya harbe mataahin da ya fito zanga zanga har lahira a jihar Bauchi ranar Litinin 5 ga wata.
Zanga zanga ta ɗauki sabon salo a jihar Osun da ma wasu sassan Najeriya a rana ta biyar watau yau Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 yayin da wasu suka fara cire kaya.
Ahmad Yusuf
Samu kari