Betta Edu Za Ta Koma Kujerar Minista? Tinubu Ya Yi Muhimman Sauye Sauye a Ma'aikatar Jin Kai

Betta Edu Za Ta Koma Kujerar Minista? Tinubu Ya Yi Muhimman Sauye Sauye a Ma'aikatar Jin Kai

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimman naɗe-naɗe a ma'aikatar jin kai da yaƙi da fatara ta tarayya
  • Hakan wata alama ce da ke nuna zai yi wahala shugaban ya dawo da Dr. Betta Edu kan kujerar minista bayan dakatar da ita a watan Janairu, 2024
  • Tinubu ya dakatar da Edu ne bisa zargin hannu a karkatar da wasu kuɗi kuma ya umarci EFCC ta gudanar da bincike kan lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ga dukkan alamu dakatacciyar ministar harkokin jin ƙai da yaƙar talauci, Dr. Betta Edu ta tafi kenan, zai wahala ta koma kan muƙaminta ba.

Tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da ita a watan Janairu bisa zargin cin hanci da rashawa ake ta samun rahotannin cewa za a iya mayar da ita bakin aiki.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A ƙarshe ƴan Arewa sun jero buƙatunsu, sun aika saƙo ga Shugaba Tinubu

Bola Tinubu da Betta Edu.
Tinubu ya yi muhimman sauye sauye a ma'aikatar jin kai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Betta Edu
Asali: Facebook

Matakan da Bola Tinubu ya ɗauka

Shugaba Tinubu ya umarci hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta binciki ma’aikatar jin ƙai karkashin Edu, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya kuma dakatar da Halima Shehu daga matsayin shugabar gudanarwa ta NSIPA da duk shirye-shiryen da ke karkashinta.

Ya kuma kafa kwamitin ministoci don gudanar da bitar ayyukan hukumar da nufin ba da shawarar yadda ya kamata a sake fasalin NSIPA.

A jiya Talata, mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya sanar cewa Tinubu ya nada mutane bakwai a hukumomin da ke karkashin ma’aikatar jin kai da yaki da fatara.

Tinubu ya yi sauye-sauye a ma'aikatar

Ngelale ya ce shugaban ƙasar ya amince da nada Dr. Badamasi Lawal a matsayin Shugaban Hukumar NSIPA.

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam ta bayyana abin da zai jawo a samu saukin farashin abinci

Sauran naɗe-naɗen sun hada da, Funmilola Olotu, shugabar tsare-tsare a ofishin kula da harkokin Safety-Net, da Aishat Alubankudi, shugabar tsare-tsare a sashin tallafawa masu ƙaramin karfi.

Sai kuma Princess Aderemi Adebowale, shugabar shirin ciyar da ɗalibai a makarantu da Malam Abdullahi Alhassan Imam, manajan shirye-shirye na ofishin raba tallafin kudi.

Ayuba Gufwan, babban sakatare na hukumar nakasassu ta tarayya da Lami Binta Adamu Bello a matsayin darakta janar ta hukumar hana fataucin Bil’adama ta ƙasa.

Kiran da shugaban kasa Tinubu ya yi

Ngelale ya ce shugaban na fafan waɗanda aka naɗa za su maida hankali wajen kai wa ‘yan Najeriya agajin da ake bukata da kuma tabbatar da ingancin shirye-shiryen jin kai da ci gaban al’umma.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.

Tinubu ya ba Aminu Masari muƙamin TETFund

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban gudanarwan TETFund.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka ranar Talata, ya ce an naɗa mambobi 6 a hukumar tarayyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262