Ahmad Yusuf
11842 articles published since 01 Mar 2021
11842 articles published since 01 Mar 2021
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa takwaransa na jam'iyyar adawa ta APM kuma gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya cancanci zama shugaban Najeriya.
Kotun sauraron karafe-korafen zaben gwamnan jihar Osun ta manna kararraki biyu da jam’iyyun APC da PDP suka shigar gabanta kan nasarar Gwamna Ademola Adeleke.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya halarci taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar APM a zaben shugaban kasa na 2027, Seyi Makinde.
Jigon APC ya zargi 'yan adawa da amfani da wata shari'a karkashin dokar neman bayanai ta Amurka (FOIA) da ta shafi Shugaba Bola Tinubu wajen neman biyan bukatu.
Wani jigo a jam'iyyar PDP, Lere Olayinka, ya ce babban zaben shugaban kasa na shekarar 2027 zai fi wa Bola Ahmed Tinubu sauƙin samun nasara fiye da zaben 2023.
Jam'iyyar APC ta yi fatali da taron da manyan jam'iyyun adawa suka gudanar a Najeriya, tana mai cewa yunƙurin haɗin gwiwar nasu ya riga ya gaza tun kafin fara aiki.
Aƙalla garuruwa 15 a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina sun zama kango babu kowa a ciki sakamakon karuwar hare-haren da 'yan bindiga a yankin.
Jarumar masana'antar shirya fina-finan Hauss ta Kannywood, Jamila Gwarzo ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a jihar Kano ranar Juma'a.
Jam'iyyar adawa ta NDC ta karyata rahotannin da ke cewa ba ta da 'yan takarar gwamna a jihohi 12 gabanin babban zaben 2027. Ta fitar da jerin sunayensu.
Ahmad Yusuf
Samu kari