Abdullahi Abubakar
7739 articles published since 28 Afi 2023
7739 articles published since 28 Afi 2023
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya fusata kan sakin wasu 'yan daba da aka yi a jihar yayin da ya ke kokarin dakile matsalar inda ya ce zai kawo karshen matsalar.
Yayin da ake daf da gudanar da zabe a jihar Edo, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi babban kamu yayin da jiga-jigan jam'iyyar PDP suka sauya sheka.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris ya gargadi malaman addinin Musulunci kan shiga harkokin siyasa inda ya bukace su da su kaucewa cin mutuncin shugabanni.
Shahararren dan jarida, Rotimi Sankore ya riga mu gidan gaskiya, Shugabar gidan rediyon, RadioNow 95.3FM, Kadaria Ahmed ta nuna alhini kan rasuwar dan jaridar.
Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya, NCS ta ce za ta bi shaidar da ta samu daga kotu kan fitaccen ɗan daudu, Idris Bobrisky wurin ajiye shi a bangaren maza.
Yayin da shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga Najeriya, gwamnatin Tarayya ta zakulo inda ya ke a kasar Kenya inda ta ce za ta dawo da shi Najeriya.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya umarci gwamnoni su fara biyan kudin rage radadi ga ma'aikata, Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya amince da biyan N35,000.
Wasu gungun matasa sun fusata yayin da suka dauki mummunan mataki kan almajiri a jihar Kano bayan zarginsa da guntule kan wani yaro mai shekaru shida.
Yayin da ake fama da matsalar ta'addanci a Najeriya, Kungiyar Dattawan Kiristoci ta ce wasu mutane ne daga kasashen ketare ke kawo matsalar tsaro a Najeriya.
Abdullahi Abubakar
Samu kari