2027: INEC Ta Cire Sunayen Mutum Miliyan 1.6 daga Rajistar Masu Zabe

2027: INEC Ta Cire Sunayen Mutum Miliyan 1.6 daga Rajistar Masu Zabe

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta cire bayanan mutum 1,609,553 daga rajistar masu zaɓe gabanin zaɓen 2027
  • Hukumar ta ce daga cikin bayanan da aka cire, 1,608,660 rajista ne marasa inganci, yayin da 873 kuma bayanan mamatan da aka tantance ne
  • Hukumar INEC ta kuma bayyana dalilin da ya sa mutanen da suka yi rajista ba su samu katin zaɓensu na dindindin (PVC) ba har yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cire bayanan mutum 1,609,553 daga rajistar masu zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce an cire bayanan ne bayan gudanar da bincike da tantance rajistar masu zaɓe.

Kara karanta wannan

Abin da mutane ke cewa bayan sun samu tallafin N50,000 daga Gwamnatin tarayya

Farfesa Joash Amupitan
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na gyara kura-kurai da kuma tabbatar da ingancin rajistar masu zaɓe kafin babban zaɓen ƙasar na 2027.

INEC ta cire mutum miliyan 1.6

Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar ta cire bayanan mutane 1,609,553, waɗanda suka haɗa da rajista 1,608,660 da aka tabbatar ba su da inganci da kuma bayanan mamatan masu zaɓe 873.

Amupitan ya ce hukumar za ta ci gaba da sanar da jama'a sakamakon binciken da za a iya tabbatarwa, tare da kare bayanan sirrin mutane da kuma mutuncin binciken da ake gudanarwa.

Punch ta rahoto ya ce:

“Mun fahimci cewa gano kura-kurai a rajistar masu zaɓe na haifar da tambayoyi kan yadda suka faru. Abin da ya dace shi ne gudanar da bincike bisa hujjoji, gyara matsalolin da aka gano da kuma ƙarfafa matakan hana sake faruwarsu.”

Magana kan karbar katin zabe

Shugaban hukumar ya kuma yi bayani kan dalilin da ya sa mutanen da suka yi rajista a kashi na uku na aikin rajistar masu zaɓe ba su samu katin zaɓensu na dindindin ba.

Kara karanta wannan

An kara wa jami'an INEC albashi da alawus yayin da ake shirin zaben 2027

Ya ce ana ci gaba da raba katunan PVC na kashi na farko da na biyu, ciki har da waɗanda suka yi sauyin rumfar zaɓe, a ƙananan hukumomi daban-daban na ƙasar.

Wajen zabe a Najeriya.
Mutane a layin kada kuri'a a Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Amupitan ya ƙara da cewa ana kuma kawo wasu katunan da aka samar a kashi na uku, kuma za a aika da su zuwa jihohi nan da mako mai zuwa.

Ya ce daga ranar 1 ga Disamba, 2026, hukumar za ta koma raba katunan a cibiyoyin rajista na yankunan zaɓe a faɗin Najeriya.

Shugaban INEC ya buƙaci waɗanda suka yi rajista a kashi na uku da su ƙara haƙuri, yana mai cewa ana samar da katunan ne a wajen Najeriya.

An nada alakalan karar zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa an ƙaddamar da alkalai 375 a ranar Litinin domin su saurari ƙararrakin zaɓe da waɗanda ba su gamsu da sakamakon zaɓe za su shigar a faɗin ƙasar.

Sashe na 285(1) da (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bai wa shugaban kotun ɗaukaka ƙara alhakin kafa kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe.

Haka kuma, sashe na 134(3)(a) da (b) na dokar zaɓe ta 2026 ya tanadi lokacin kafa kotunan da kuma buɗe ofisoshinsu domin karɓar ƙararraki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng