Ana Fargabar Rasa Rai Yayin da Miyagu Suka Farmaki Ɗan Takarar Gwamna

Ana Fargabar Rasa Rai Yayin da Miyagu Suka Farmaki Ɗan Takarar Gwamna

  • Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar Edo, miyagu sun farmaki dan takar gwamna a jihar
  • Bata garin sun farmaki Olumide Akpata da ke neman takara a jam'iyyar LP a ranar Juma'a 12 ga watan Afrilu
  • Dan takarar ya bayyana cewa ya na da tabbacin cewa wani daga jami'an gwamnatin jihar ne ya dauki nauyinsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Wasu bata gari sun farmaki dan takarar gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar LP, Olumide Akpata.

Akpata ya zargi babban jami'in gwamnatin jihar da daukar nauyin harin da aka kai masa a Jami'ar Benin, cewar Punch.

Miyagu sun kai hari kan ɗan takarar gwamna ana daf da zaɓe
Miyagu sun kai hari kan ɗan takarar gwamna a jami'yyar LP, Olumide Akpata a Edo. Hoto: Lauretta Onochie, Getty Images.
Asali: Twitter

Yaushe aka kai hari kan ɗan takarar?

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a 12 ga watan Afrilu a cikin Jami'ar yayin wani babban taro, cewar New Telegraph.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar ya bayyyyana cewa harin ya rutsa da wani lakcara a Jami'ar inda yanzu haka ya ke karbar kulawa a asibiti.

"Wani daga cikin ma'aikata na ya nuna min wani faifan bidiyo da wani ke cewa jami'an tsaro sun harbe shi."
"Naso ace mutumin ya nuna fuskarsa domin tabbatar da gaskiyar lamarin, mun taru da manyan lakcarori a Jami'ar domin tattaunawa ta musamman."
"Abin mamaki sai wasu bata gari suka tarwatsa taron da cewa ba za a gudanar da taron ba tare da sanin su a matsayinsu na dalibai, kowa ya yi mamaki har da farfersoshin da ke wurin."

- Olumide Akpata

Ya zargi 'yan siyasa da kisa harin

Akpata ya ce sai da ya samu taimakon jami'an tsaro kafin ta tsira daga harin ya samu ya fita daga cikin jami'ar.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya dauki zafi bayan sakin 'yan daba daga kulle, ya sha alwashi kan lamarin

Ya ce sun san meye ya ke faruwa saboda lokacin siyasa ne akwai tsoffin 'yan siyasa da wayonsu ya kare sai dai ta wannan hanya.

Jiga-jigan PDP sun koma APC a Edo

A wani labarin, ana daf da gudanar da zabe a jihar Edo, wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Edo.

Daga cikin wadanda suka sauya shekan akwai tsohon sanata da kuma tsohon dan majalisar tarayyar da sauran manya-manyan jam'iyyar a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel