Kaduna: Mataimakiyar Gwamna Uba Sani Ta Yi Babban Rashi a Rayuwarta

Kaduna: Mataimakiyar Gwamna Uba Sani Ta Yi Babban Rashi a Rayuwarta

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi ta’aziyyar rasuwar Alhaji Abubakar Mohammed, mahaifin mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe
  • Marigayin ya shafe sama da shekaru 60 yana aikin gwamnati, inda ya fara a matsayin malamin makaranta a shekarar 1960
  • Ya taba zama kwamishinan zaɓe a jihar Oyo a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi ta’aziyyar rasuwar mahaifin mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, mai suna Alhaji Abubakar Mohammed.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin saƙon ta’aziyyar da ya fitar ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2026, inda ya jajanta wa mataimakiyarsa da iyalanta.

Uba Sani ya jimamin mutuwar mahaifin mataimakiyarsa
Gwamna Uba Sani da marigayi Alhaji Abubakar Mohammed. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: Facebook

Uba Sani, wanda ya yi magana a shafin Facebook a madadin gwamnatin jihar Kaduna da al’ummarta, ya ce yana tare da iyalan marigayin a wannan lokaci na jimami.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fitar da sanarwa ga shugabannin ADC da aka rusa takarar Atiku

Saƙon ta’aziyyar Uba Sani

Gwamnan ya bayyana cewa rasuwar mahaifi babban rashi ne da kalmomi ba za su iya bayyana girman radadinsa ba.

Ya ce:

“A madadin gwamnatin jihar Kaduna da al'ummarta, ina mika ta’aziyyata ga mai girma mataimakiyar gwamna, iyalanta da duk wadanda rasuwarsa ta shafa.
“Muna tare da su a cikin wannan bakin ciki, kuma muna saka su cikin addu’o’inmu a wannan lokaci mai wahala.”

Haka kuma, Uba Sani ya roƙi Allah SWT Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

Ya kara da cewa yana fatan iyalan za su samu kwanciyar hankali ta hanyar tunawa da kyawawan abubuwan da suka yi tare da marigayin da kuma tarbiyyar da ya ba su.

An yi babban rashi a jihar Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna. Hoto: Senator Uba Sani.
Source: UGC

Tarihin aikin mahaifin mataimakiyar gwamnan Kaduna

Alhaji Abubakar Mohammed ya kasance tsohon ma’aikacin gwamnati kuma jami’in harkokin ilimi da ya fara aikinsa a matsayin malamin makaranta a shekarar 1960.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara karewa: Gwamna Radda ya fadi yadda zai dakile matsalar tsaro

Daga baya, ya zama jami’in ilimi a karamar hukumar Jama’a, kafin daga bisani ya rike mukamin shugaban karamar hukumar Sanga.

Haka kuma, marigayin ya taba zama kwamishinan zaɓe na hukumar INEC a jihar Oyo a lokacin mulkin tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha.

A wata hira da jaridar The Sun ta yi da shi a shekarar 2020, Mohammed ya bayyana samun da 'yarsa ta yi na zama mataimakiyar gwamna a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka fi faranta masa rai a rayuwa.

Ya ce ya fice daga jam’iyyar PDP domin mara mata baya bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zabe ta a matsayin abokiyar takararsa a zaben gwamna na shekarar 2019.

A cewarsa, bai son ya samu kansa a matsayin wanda ke adawa da 'yarsa a siyasa.

Uba Sani ya ari bakin gwamnonin Arewa

Mun ba ku labarin cewa Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu 100%.

Gwamnonin sun bayyana cewa wajibi ne Arewa ta mutunta yarjejeniyar karba karba da ta yi da Kudu tun a shekarar 1999.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce yarjejeniyar ta tanadi cewa Arewa za ta yi wa’adi biyu a jere, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.