ICPC Ta Yi Gyaran Tuhume Tuhume, Ta Kara Sunayen Mutum 4 a Shari'ar Kafa Hukumar Bogi
- Hukumar ICPC ta ƙara yawan tuhume-tuhume da take wa shugaban hukumar bigi, Adeniyi Adeyemi daga 22 zuwa 36
- Ana zargin wasu ma’aikatan sun taimaka wajen gudanar da hukumar bogi da shigar da ita cikin kasafin kuɗin Najeriya
- Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 18 ga Nuwamba saboda ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma ba ta halarci zaman ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuffukan da suka Shafi Hakan (ICPC) ta shigar da sabsbbin tuhume-tuhume kan shugaban hukumar bogi (PFIPC), Adeniyi Adeyemi.
An gurfanar da Adeyemi ne kan zargin jagorantar kafa hukumar Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) ba tare da izini ba.

Source: Twitter
Premium Times ta rahoto cewa ICPC ta ƙara yawan tuhume-tuhumen da take yi wa Adeyemi daga 22 zuwa 36, tare da haɗa wasu mutum huɗu a cikin waɗanda ake tuhuma a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
ICPC ta kara yawan tuhume-tuhume
Sababbin waɗanda ake tuhumar ma’aikatan gwamnati ne daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ofishin Babban Akanta na Tarayya da kuma Ma’aikatar Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki ta Tarayya.
Ana zargin mutanen sun taka rawa wajen taimakawa hukumar bogin ta gudanar da ayyukanta tare da shigar da ita cikin kasafin kuɗin Najeriya.
Sunayen mutanen sun haɗa da Aminu Abdullahi, Harry Ogaba, Florence Omameh da Patricia Akhigbe.
Wannan shi ne karo na biyu da ICPC ta yi wa tuhume-tuhumen kwaskwarima tun bayan da ta karɓi jagorancin shari’ar a watan jiya. Tun da farko dai ’yan sandan Najeriya ne suka shigar da ƙarar a bara.
Abin da ya kawo cikas a kotu
Lauyan masu gabatar da ƙara, Sylvanus Tahir (SAN), ya sanar da kotun sabon sauyin da aka samu a ranar zaman yau Litinin.
An shirya zaman kotun na ranar Litinin ne domin sauraron buƙatar neman beli da Adeyemi ya gabatar, amma aka dakatar da shari’ar saboda an yi wa tuhume-tuhumen kwaskwarima.
Sai dai zaman ya gamu da cikas saboda Omameh, wadda ita ce ta huɗu cikin waɗanda ake tuhuma, ba ta halarci kotu ba bisa dalilin rashin lafiya. Sauran waɗanda ake tuhumar sun halarci zaman.
Tahir ya bayyana cewa shari’ar ta koma “shari’ar haɗin gwiwa da ta ƙunshi mutum biyar da ake tuhuma.”
Saboda haka, ya buƙaci kotun ta ɗage shari’ar na ɗan lokaci domin Omameh ta samu damar murmurewa ta kuma bayyana amsarta kan tuhume-tuhumen.
Lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, SAN, bai nuna adawa da buƙatar ba, amma ya tunatar da kotun cewa an daɗe ana tsare da wanda yake karewa.
Kotun ta ɗage shari’ar
Alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Halilu Yusuf, ya amince da buƙatar ɗage zaman kotun, inda ya sanya ranar 18 ga Nuwamba domin karɓar amsoshin waɗanda ake tuhuma kan tuhume-tuhumen.
Alƙalin ya kuma bayar da umarnin mayar da Adeyemi zuwa gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, yayin da sauran waɗanda ake tuhuma za su koma wurin da ICPC ke tsare da su.
Dalilin ICPC na wanke Gbajabiamila
Kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (ICPC) ta ce ba ta gano wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya san da zaman PFIPC ba.
Binciken ya nuna cewa Adeyemi ne ya ƙirƙiri takardar nadin kansa tare da amfani da takardar kai ta fadar shugaban ƙasa da sa hannun Gbajabiamila.
Asali: Legit.ng

