INEC Ta Yi Magana kan Fito da Takardun Tinubu da Soke Takarar Atiku a Zaben 2027
- Hukumar INEC ta ce har yanzu ba ta samu kwafin sahihin hukuncin kotu kan rikicin shugabancin ADC da takardun takarar Shugaba Bola Tinubu ba
- Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya ce ba sa daukar mataki bisa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta sai sun samu takardun doka
- Farfesa Amupitan ya tabbatar da cewa zai yi duk abin da ya dace da zarar kwafin takardun kotu ya isa ofishinsa a hukumance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce har yanzu ba ta samu kwafin sahihan takardun hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC ba.
Haka zalika, iNEC ta tabbatar da cewa ba a kawo mata sahihiyar takardar umarnin kotu na gabatar da shaida kan takardun karatun Shugaba Bola Tinubu ba.

Source: Facebook
Premium Times ta ce shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai kan rajistar masu kada kuri’a da aka gudanar a Abuja ranar Litinin.
Amupitan ya yi magana kan takarar Atiku
Da yake amsa tambayoyi kan hukuncin kotun da ya soke takarar Atiku Abubakar, da shugabancin ADC karkashin David Mark, Amupitan ya ce hukumar INEC ba ta daukar mataki bisa rahotannin da ake yadawa, sai dai tana bukatar sahihan takardun doka.
“Ya zuwa yau, ban samu kwafin sahihin hukuncin Babbar Kotun Tarayya ba, saboda ba ma daukar mataki kawai bisa abin da ake wallafawa a kafafen sada zumunta.
“Na tuna wani hukunci da Kotun Koli ta yanke a wani lokaci da ya gabata, inda aka wallafa wani abu a kafafen sada zumunta, ya yadu sosai, amma daga baya Kotun Kolin ta nesanta kanta da shi, lamarin da ya kai ga gudanar da bincike,” in ji shi.
Ya bayyana cewa idan hukumar ta samu irin wannan hukunci, ana fara mika shi ga shugaban INEC, wanda daga nan yake neman shawarar kwararru daga sashen da abin ya shafa kafin a gabatar da shi domin nazari.
INEC na dakon umarnin kotu
Dangane da hukuncin kotu da ya umarce shi da ya gabatar da takardun takarar Tinubu, Amupitan ya ce zai dauki matakan doka da suka dace ne bayan an mika masa umarnin kotun a hukumance.

Source: Getty Images
A rahoton jaridar Daily Trust, Farfesa Amupitan ya ci gaba da cewa:
“Ban samu umarnin ba. Don haka, idan na samu, zan duba abin da umarnin ya kunsa, sannan in san matakin da ya kamata in dauka,” in ji shi.
Umarnin kotu kan takardun Tinubu
Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci shugaban INEC, Joash Amupitan, ya gabatar da takardun takarar Shugaba Bola Tinubu na 1999 da 2023.
Kotun ta kuma umarci Amupitan ya gurfana a matsayin shaida a shari’ar Omoyele Sowore, wanda DSS ke tuhuma kan wasu saƙonnin da ya wallafa, inda ya kira Tinubu da "babban mai laifi."
Wannan mataki ya biyo bayan matsayar da kotun ta dauka, inda ta amince da buƙatar masu kare Sowore na gayyatar Amupitan da Joe Igbokwe, tsohon sakataren yaɗa labarai na APC a Legas.
Asali: Legit.ng

