Kotun daukaka kara ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar sauke Buhari da nada Atiku

Kotun daukaka kara ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar sauke Buhari da nada Atiku

  • Wata kotun daukaka kara a Abuja ta saka ranar sauraron daukaka karar CSOCLC, kungiyar da ke bukatar a tuge Buhari daga shugabancin kasa
  • A ranar 22 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa, kotu za ta duba bukatar kungiyar kuma idan ta amince, Atiku Abubakar zai zama shugaban kasa
  • Tun farko wata babbar kotun tarayya ta yi fatali da bukatar kungiyar na kwace mulki daga hannun Buhari saboda rashin takardun makaranta

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta saka ranar 22 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa a matsayin ranar da za ta saurari karar da ke bukatar soke zaben Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, Daily Trust ta wallafa.

Kungiyar Incorporated Trustees of the Civil Society Observatory for Constitutional and Legal Compliance (CSOCLC) ta ce idan kotun ta aminta da bukatar ta, ta bada umarnin rantsar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin shugaban kasa tunda shi ne ya zo na biyu a zaben.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya gana da Fasto Tunde Bakare a fadar shugaban kasa

Kotun daukaka kara ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar sauke Buhari da nada Atiku
Kotun daukaka kara ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar sauke Buhari da nada Atiku. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Kwamitin masu shari'a uku da ya samu shugabancin Mai shari'a Peter Ige, yayin sauraron, sun umarci cewa a mika takardun kotun gaban hukumar zabe mai zaman kanta, jam'iyyar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lauyan masu daukaka karar, Nnamdi Ahaiwe ya sanar da kotun cewa wadanda ake karar, wadanda suka bayyana gaban kotun a ranar 14 ga watan Janairun da ta gabata sun karba takardun.

Amma mai shari'a Ige ya ce, "A sake mika musu takardun. Shari'a ta bukaci mu ga asalin takardun."

Kungiyar farar hulan ta garzaya gaban kotun daukaka karar inda ta ke kalubalantar hukuncin babbar kotun da ta yi watsi da bukatarsu ta kalubalanci zaben.

Kungiyar ta ce a cikin takardun Buhari akwai takardar rantsuwar karya wacce ta ce sakamakon karatunsa su na tare da sakataren majalisar rundunar soji, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Sojoji 4 sun sheka lahira, 1 ya jigata yayin arangama da 'yan ISWAP a Borno

A wani labari na daban, a kalla sojoji hudu ne suka rasa ran su a ranar Talata yayin bankado harin da mayakan ISWAP suka kai garin Ngamdu, wani gari da ke tsakanin iyakar jihohin Yobe da Borno.

PRNigeria ta tattaro cewa, majiya mai karfi daga rundunar ta ce harbin ya samu hafsan sojan ne yayin da ya ke kokarin bai wa bataliyarsa kariya daga 'yan ta'addan.

An ruwaito cewa hafsan sojan ya samu miyagun raunika. Amma kuma an kai shi asibitin sojoji inda ya ke samun sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel