Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton
Kasancewa dan Najeriya mai matsayi na biyu tabbas ya zarce batun mallakar takardun shaidar karatu, kwarewar siyasa, da gogewa a fagen jagorancin kasa. Hakanan, hadawa da karfin iya motsa jiki a na daga cikin jerin halayen da ake bukata.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Asabar, 16 ga watan Oktoba, ya tabbatar wa da duniya cewa shi mutum ne da ya cancanci ofishin sa ta fuskar karfin jiki.
Mataimakin shugaban kasar ya yi maraba da gasar Baton na Sarauniya Elizabeth a gasar Commonwealth ta Birmingham ta 2022 a fadar gwamnati da ke Abuja.
A daya daga cikin hotunan da hadimin shugaban kasa Buhari Sallau ya yada a shafinsa na Facebook, an ga Osinabjo yana gudu da sandar wasan tare da wasu jami'an gwamnati ciki har da ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare.
Sallau yace Osinbajo ya karbi sandar ne a madadin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasanni: Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle
A wani labarin, Kungiyar kwallon kafa mai buga Firimiya a kasar Ingila, Newcastle United ta koma hannun wata kungiyar da Saudiyya ke marawa baya, Al-Jazeera ta ruwaito.
Kungiyar ta Newcastle United ta amince da cinikin bayan wasu takardun doka sun tabbatar da cewa kasar ba za ta yi tasiri kan harkoki ko iko da kungiyar ba.
A cewar sanarwar Firimiya:
"Kungiyar Gasar Firimiya, Newcastle United Football Club da St James Holdings Limited sun warware takaddamar da ake yi kan karbe kungiyar daga hannun PIF, PCP Capital Partners da RB Sports & Media"
Asali: Legit.ng