Zargin alaka da yan binidiga: Dan Majalisa ya bayyana abinda yasa aka dakatar dashi a Zamfara

Zargin alaka da yan binidiga: Dan Majalisa ya bayyana abinda yasa aka dakatar dashi a Zamfara

  • Honorabul Muhammad Yusuf, mai wakiltar Anka a majalisar dokokin Zamfara ya musanta zargin da ake masa na alaƙa da yan bindiga
  • Dan majalisan, wanda yana ɗaya daga cikin mutum biyu da aka dakatar Ranar Talata, yace a shirye yake ya rantse da Alƙur'ani
  • A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da wasu yan majalisu biyu bisa zargin murna da sace mahaifin kakaki

Zamfara - Ɗaya daga cikin mambobi biyu da majalisar dokokin jihar Zamfara ta dakatar, Muhammad Yusuɗ, ya musanta zargin da ake masa na alaka da yan bindiga, kamar yadda Premium times ta rahoto.

Honorabul Muhammad ya kuma musanta zargi na biyu da ake masa cewa ya yi farin ciki da aka sace mahaifin kakakin majaisar jiha.

Kara karanta wannan

Ba guduwa zan yi ba: Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnatin Buhari da hana shi sakat

Dan majalisan mai wakiltar Anka ya bayyana cewa kakakin majalisa, Nasiru Magarya, shine ya yi ruwa yayi tsaki wajen dakatar dashi domin ya wargaza shirinsu na tsige shi.

Jihar Zamfara
Zargin alaka da yan binidiga: Dan Majalisa ya bayyana abinda yasa aka dakatar dashi a Zamfara Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

Ya kuma kara da cewa manyan yan siyasar jihar sun masa barazana kan shirin da suke na tsige kakakin majalisar dokokin.

Gwamna Matawalle ya sansanta tsakani

A cewar Muhammad bai yi wata-wata ba ya sanar da gwamna Bello Matawalle shirin mambobin majalisa na tsige kakaki.

Yace:

"Bayan sanar da shi, gwamna ya turo tsohon minsitan kudi, Bashir Yuguda, domin ya yi sasanci, wanda sanadin haka masu shirin suka aje makamansu."

Zan rantse da Alkur'ani?

Dan majalisar yace ya yi matukar mamaki da ya samu labarin an dakatar da shi lokacin yana Kano, inda yaje halartar taron UNICEF.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

"Ina ƙalubalantar wanda ya kai kudirin, Yusuf Kanoma, ya fito bainar jama'a mu rantse da littafi mai tsarki (Alkur'ani) kan cewa kowa yana da gaskiya."
"Muna fatan kwamitin da aka dora wa ragamar bincike zai mana adalci da ni da kuma ɗan uwana da aka zarga."

Honorabul Muhammad ya tabbatar da cewa lokacin da aka sace mahaifin kakakin majalisa, na kira shi a wayar salula domin jajanta masa.

A wani labarin na daban kuma Peter Obi ya maida zazzafan martani kan maƙudan kudin da Buhari ya ware wa ofishin matarsa Aisha Buhari

Obi yace babu ofishin matar shugaban ƙasa a kundin tsarin mulki, kuma akwai ɓangarorin da suka fi nan muhummanci.

Tsohon gwamnan ya kuma alakanta matsalar tsaron Najeriya da rashin aikin yi da matasa ke fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel