Peter Obi ya maida zazzafan martani kan maƙudan kudin da Buhari ya ware wa ofishin matarsa Aisha Buhari

Peter Obi ya maida zazzafan martani kan maƙudan kudin da Buhari ya ware wa ofishin matarsa Aisha Buhari

  • Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi kaca-kaca da kasafin kuɗin da Gwamnatin Buhari ta ware wa Ofishin Aisha
  • Obi yace babu ofishin matar shugaban ƙasa a kundin tsarin mulki, kuma akwai ɓangarorin da suka fi nan muhummanci
  • Tsohon gwamnan ya kuma alakanta matsalar tsaron Najeriya da rashin aikin yi da matasa ke fama da shi

Lagos - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya nuna ƙin amincewarsa da kasafin kuɗin da aka ware wa ofishin matar shugaban ƙasa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya bayyana abubuwan da aka ware za'a yi a ofishin da marasa amfani, wanda ya kamata a karkatar da su zuwa wani ɓangare mai amfani.

Obi ya yi wannan furuci ne a wurin taron shekara-shekara karo na 8 a cocin Foursquare Gospel, a matsayinsa na babban bako mai jawabi.

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

Peter Obi
Tsohon Gwamna ya maida zazzafan martani kan maƙudan kudin da kasafin 2022 ya ware wa ofishin Aisha Buhari Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

A cewarsa kasafin kuɗin da aka warewa ofishin na Aisha Buhari, ya kamata a dakatar da shi saboda ƙarin hanyoyin kashe kuɗi masu muhimmanci a Gwamnati.

Wane ɓangare ya kamata akai kasafin kuɗin?

Obi, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan ƙaruwar matsalar tsaro da kuma zaman kashe wando da matasa ke yi, yace kamata ya yi ayi amfani da kuɗaɗen a ɓangaren ilimi da lafiya.

A cewarsa, ofishin matar shugaban ƙasa, wanda ba shi a kundin tsarin mulki, ana cigaba da gudanar da shi da kuɗaɗen al'umma a matakin ƙasa, jiha da na kananan hukumomi.

"Matan shugaban ƙasa, gwamnoni harda da na shugabannin ƙananan hukumomi, babu wata takarar zaɓe da suka tsaya har aka zaɓe su. To dan me ake cigaba da gudanar da ofishin?"

Kara karanta wannan

Matar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta yi magana mai muhimmanci kan Matan Gwamnoni

"Muna fama da ƙarancin kudin shiga, ga ciwo bashi domin cike gurbin kasafin kuɗi ga matasa babu aikin yi."

Dalilin da yasa matsalar tsaro ke kara ruruwa

Obi ya alaƙanta ruruwar matsalar tsaron ƙasar nan da rashin aikin yin da matasan yan Najeriya suke fama da shi.

A wani labarin kuma Abubuwan da ya kamata ku sani game da sakonnin da ake yaɗawa a dandalin WhatsApp

A kwanan nan duk mai amfani da dandalin sada zumunta na Whatsapp to ya gamu da ɗaya daga cikin waɗannan sakonnin da zamunyi bayani a kai.

Mutane na ta kokarin turawa abokanan su sakonnin duk da cewaɓbasu da hujjar kare kansu cewa dokokin daga WhatsApp suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel