Sojoin Najeriya sun hallaka kasurgumin dan bindiga da yayi tuban muzuru, Alhaji Karki

Sojoin Najeriya sun hallaka kasurgumin dan bindiga da yayi tuban muzuru, Alhaji Karki

  • Alhaji Karki ya gamu da ajalinsa hannun jami'an tsaron Najeriya
  • Karki a baya ya tuba kuma yayi alkawarin daina satar mutane amma kuma ya koma daji
  • Gwamnatoci sun katse layukan sadarwa don kawar da tsagerun yan bindiga

Neja - Dakarun Sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka kasurgumin dan bindiga, Alhaji Karki, yayinda yake kokarin kai musu hari a jihar Neja.

Alhaji Karki, wanda yayi tuban muzuru bayan mika wuya ya koma daji don cigaba da addaban al'ummar jihar Neja kuma ya jagoranci kisa da garkuwa da mutane da dama.

Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyana cewa "dan bindigan na da yara da makamai barkatai."

Tsohon Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Sani Usman, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook idan yace:

"Majiyoyi daga Neja sun tabbatar da kisan kasurgumin shugaban yan bindiga Alhaji Karki a jihar Neja yayinda yake kokarin kaiwa sansanin Soji hari."

Kara karanta wannan

Ganduje ya mayar da martani kan yan majalisan da suka kai kararsa Abuja, Kabiru Gaya ya zame kansa

"Kisan wannan dan bindiga alamun nasara ne na yaki da yan bindiga."

Sojoin Najeriya sun hallaka kasurgumin dan bindiga da yayi tuban muzuru, Alhaji Karki
Sojoin Najeriya sun hallaka kasurgumin dan bindiga da yayi tuban muzuru, Alhaji Karki
Asali: UGC

Gwamna ya gargaɗi Alkalai da Lauyoyi kan tsayawa yan bindigan da aka damke a Kotu

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya gargaɗi alkalai da lauoyi kan bada belin yan bindiga da sauran yan ta'adda da aka cafke a jihar.

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a wurin taron rantsar da sabbin alƙalai uku a gidan gwamnati dake cikin garin Ƙatsina, kamar yadda This day ta ruwaito.

Masari yace ya zama wajibi a hukunta yan bindiga, yan fashi da sauran masu aikata manyan laifuka domin ya zama izina ga sauran mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel