Gwamna ya gargaɗi Alkalai da Lauyoyi kan tsayawa yan bindigan da aka damke a Kotu

Gwamna ya gargaɗi Alkalai da Lauyoyi kan tsayawa yan bindigan da aka damke a Kotu

  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya gargaɗi alkalai da lauyoyi kan samarwa yan ta'adda beli
  • Masari yace mambobin kungiyar lauyoyi ta ƙasa na amfani da dokar yanci wajen kubutar da yan ta'adda maimakon a hukunta su
  • Ya kuma yi kira ga Alƙalai su yi amfani da mukamansu wajen tabbatar da anyi adalci a ɓangaren shari'a

Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya gargaɗi alkalai da lauoyi kan bada belin yan bindiga da sauran yan ta'adda da aka cafke a jihar.

Gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne a wurin taron rantsar da sabbin alƙalai uku a gidan gwamnati dake cikin garin Ƙatsina, kamar yadda This day ta ruwaito.

Masari yace ya zama wajibi a hukunta yan bindiga, yan fashi da sauran masu aikata manyan laifuka domin ya zama izina ga sauran mutane.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Gwamna Aminu Bello Masari
Gwamna ya gargaɗi Alkalai da Lauyoyi kan tsayawa yan bindigan da aka damke a kotu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Alkalai suna haɗa kai da lauyoyi - Masari

Gwamnan ya ƙara da cewa mambobin ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) suna haɗa kai da wasu alkalai ta ƙaraƙashin ƙasa domin su kuɓutar da yan ta'adda da yan fashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar gwamna Masari mambobin NBA da kuma wasu alƙalai suna amfani da dokokin yancin ɗan adam wajen sakin yan ta'addan maimakon hukunta su.

Masari yace:

"Wajibi NBA ta dawo da mambobinta kan hanya, waɗanda ke amfani da dokokin yancin ɗan adam wajen kuɓutar da yan ta'adda."
"Muna da misalai da dama, inda aka saki yan bindiga, yan fashi ta hanyar yancin ɗan adam, ba dan komai ba sai don su cigaba da aikaita wannan laifin."

Dole mu haɗa kai don fuskantar matsalolinmu

Masari ya ƙara da cewa, "Muna cikin wani yanayi mai matukar wahala na kalubalen tsaro, saboda haka wajibi mu haɗa kan mu wajen kawo ƙarshen lamarin."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

Daga ƙarshe Masari ya roki sabbin lauyoyin da su yi amfani da damar da Allah ya basu wajen tabbatar da an yi adalci a shari'o'in jihar.

A wani labarin na daban Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina

Mukaddashin shugaban NCS reshen Katsina, Wada Chide, yace mutane na amfani da abun hawansu wajen siyo fetur su juye a jarkokin.

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar musamman waɗanda ke zaune a kauyukan dake bakin boda su cigaba da kiyaye doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262