Abin al'ajabi: Bidiyon yadda wani mutum ya yi tafiya a kan kwai ba tare da sun fashe ba

Abin al'ajabi: Bidiyon yadda wani mutum ya yi tafiya a kan kwai ba tare da sun fashe ba

  • A kwanan nan ne wani bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta inda aka ga wani mutumi yana tafiya a kan kiretan kwai a cikin wata mota amma kuma babu ko guda da ya fashe
  • Mutumin ya ba masu amfani da shafin soshiyal midiya da dama mamaki domin ba za su iya bayanin yadda aka yi ya iya tafiya a kan kwan ba tare da sun fashe ba
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun tofa albakacin bakunansu kan bidiyon yayin da wasu ke mamakin dalilin da yasa ya zabi bi ta kan kwan bayan akwai fili a cikin motar

Wani bawan Allah ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a kafafen sada zumunta bayan an gano shi yana tafiya a kan kiretan kwai ba tare da ko daya ya fashe ba.

Read also

Hadimin da Ganduje ya sallama daga aiki yace burki ya tsinkewa Gwamnan jihar Kano

A cikin bidiyon da shafin @ijeomadaisy ya yada a Instagram, ana iya ganin mutumin yana loda kwai a cikin babbar mota. Yayin da yake ɗauke da kiretan ƙwai a hannunsa, don lodawa a cikin motar, mutumin ya yi tafiya a kan waɗanda aka riga aka loda a cikin motar.

Abin al'ajabi: Bidiyon yadda wani mutum ya yi tafiya a kan kwai ba tare da sun fashe ba
Mutumin ya ba mutane da dama mamaki Hoto: @ijeomadaisy
Source: Instagram

Shafin @ijeomadaisy ya rubuta:

"Shin akwai wanda zai iya bayanin yadda aka yi ya iya tafiya akan kiretan ƙwai ba tare da an samu ko guda daya da ya fashe ba?"

Yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi mamaki bayan kallon bidiyon kuma wasu daga cikinsu sun yi barkwanci game da shi saboda ba za su iya bayanin yadda aka yi mutumin ya iya tafiya akan kwan ba tare da sun fashe ba.

Read also

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

Da yake mayar da martani, wani mai amfani da Instagram mai suna @momingathome ya ce:

"Dole ne ma sai yayi tafiya akan ƙwan ?? Duk wannan sarari da ƙafarsa zata iya shiga, bai yi tafiya a can ba, abegy."

@em_uko yayi sharhi:

"Muddin an jera ƙwan suna kallon sama ba gefe ba zasu iya tsagewa ba."

@mubbyfabrics ya ce:

"Wannan ba tsafi bane kuwa?"

Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce

A wani labarin, hotunan wani babur dauke da mutane takwas a lokaci daya ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta yayinda mutane da dama suka samu abin fadi.

Babban abunda mutane ke tambaya shine: Me zai sa mutum ya kai ga mayar da babur din aka kera don daukar akalla fasinjoji biyu zuwa na daukar mutum takwas?

Mabiya shafin soshiyal midiya din sun kara da cewa mayar da babur din zuwa hakan ba tare da kara karfin injin din ba yana iya zama mai matukar hatsari.

Read also

Bidiyon saurayin da ya bata rai bayan budurwar da ya gayyata cin ‘Pizza’ ta zo da wasu kawayenta biyu

Source: Legit Nigeria

Online view pixel