Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce

Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce

- Hotunan wani babur da aka sake fasalin sa ya sa mutane da dama fadin albarkacin bakunansu a shafin Twitter

- Bayan an sake kera ta, babur din ta mallaki doguwar kujera wanda zai iya daukar fasinjoji bakwai baya ga matukin ta

- Mutane da dama da suka ga hotunan sun nuna matukar damuwar su game da hatsarinsa, sun bayyana cewa ba a yi injin din don daukar irin wannan wahalar ba

Hotunan wani babur dauke da mutane takwas a lokaci daya ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta yayinda mutane da dama suka samu abin fadi.

Babban abunda mutane ke tambaya shine: Me zai sa mutum ya kai ga mayar da babur din aka kera don daukar akalla fasinjoji biyu zuwa na daukar mutum takwas?

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Gwamnatin Najeriya za ta gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 1.3

Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce
Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce Hoto: @Gidi_Traffic
Asali: Twitter

Mabiya shafin Twitter din sun kara da cewa mayar da babur din zuwa hakan ba tare da kara karfin injin din ba yana iya zama mai matukar hatsari.

Hotunan da aka wallafa ya nuna cewa an sake kera kujerar babur din ne. Domin ba fasinjoji damar walawa, an kuma kera wajen sa kafa mai tsawo ta yadda fasinjojin ba za su daura kafarsu a kan salansar babur din ba.

Sai dai kuma, ya kamata a lura cewa a daidai lokacin kawo wannan rahoton, Legit.ng ba za ta iya bayar da tabbaci a kan daukar hotunan ba.

Kalli wallafar a kasa:

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso ya soki yunkurin gwamnatin Ganduje na ciyo bashin N20bn domin gina gada a Kano

Ga wasu daga cikin martanin jama’a:

@Horlufemi ya ce:

"Wannan ba lafiya bane. Karamar motar bas (Korope) tafi kyau da aminci fiye da wannan takunkumin. Tsaron lafiya na gaba da komai.”

@SimpuLahgahdhas ya ce:

"Tayar ce za tafi shan wahalar."

@slimking44 ya ce:

"Don Allah kar a bar masu waldan naija su ga wannan."

A wani labarin, wani gajeren bidiyon Aliko Dangote yana jawabi ga wasu ma'aikatansa ya bazu. Kamar yadda ma'abocin amfani da Twitter mai suna Omasoro Ali Ovie ya wallafa, jama'ar duk ma'aikatansa ne na sabon kamfanin takin zamanin da ya bude.

Ya ce an yi ganawar ne yayin da ake gwada samar da takin zamanin karo na farko.

A sanye da takunkumin fuska, ma'aikatan sun nuna jin dadinsu a kan kalaman Dangote inda suka koma ayyukansu kan na'urori masu kwakwalwa dake gabansu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng