Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

  • Gwamna Hope Uzodimma ya nemi fushin Allah a kan wadanda ke da hannu a lamarin da ya kai ga kashe-kashe da kone-konen gidaje a garin Izombe
  • Har ila yau, gwamnan da ya fusata ya sha alwashin cewa sai an tona asirin wadanda suka aikata wannan danyen aikin sannan a gurfanar da su a gaban kuliya
  • A halin da ake ciki, gwamnan ya yi alƙawarin taimakawa al'umma wajen sake gina gidajensu da aka lalata

Imo - Da yake nuna bacin rai a kan kashe jami’an tsaro da lalata dukiya mai yawa a Izombe da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo a karshen mako, Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin cewa za a tona asirin wadanda suka aikata wannan ta’asar kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta kafa Kwamitin Bincike wanda zai binciki musabbabin rikice-rikicen nan da nan da kuma bayar da shawarwarin da za su taimaka wajen hana faruwar hakan a gaba.

Gwamnan ya ce ya zubar da hawaye bayan ya zagaya don gane wa idanunsa irin barnar da aka yi, jaridar Vanguard da Daily Post suka ruwaito

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan
Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan Hoto: Hope Uzodimma
Asali: Facebook

Da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Litinin tare da rakiyar hukumomin soji da na 'yan sanda, Gwamnan ya nuna bacin ransa kan mummunan lamarin.

Musamman yanayin da 'yan bindiga suka tunkari jami’an sintiri na Soja, suka kona motarsu, suka sace tare da kashe sojoji biyu, sannan suka yi awon gaba da bindigoginsu.

Gwamna Uzodimma ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya rantsar da shugabannin gudunarwa a kananan hukumomi 14

"Abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan sun fito da umurnin Jiha ta baya cewa kowa, komai girman matsayin mutum, wanda ke da kowane makami ya mayar da shi ga hukumomin tsaro.
"Abin takaici lokacin da aka bayar don wannan ya wuce. Saboda haka, duk wanda ke ajiye da ko wani makami yana cikin haɗarin kamawa da gurfanar da shi gaban shari'a."

Ya yi gargadi:

"Gwamnati za ta fita don aiwatar da wannan umurnin sosai tare da tabbatar da cewa an gano duk 'yan ta'adda a duk inda suke, kuma a hukunta su."

Gwamna Uzodimma ya ce yanzu ba abin yafewa bane ga mutane su dauki doka a hannunsu, yana mai nadamar cewa fashi da makami, tashin hankali, garkuwa da mutane da sauran nau’ukan laifuka na karuwa tun lokacin da aka fasa gidan yari a Owerrri.

Gwamnan ya mika ta'aziyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu a rikicin yayin yi wa kasarsu hidimar sannan ya ba da tabbacin cewa ba za a bari mutuwarsu ya tafi a banza ba.

Kara karanta wannan

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Ya sake nanata cewa Gwamnati za ta yi duk abin da za ta iya don tallafawa hukumomin tsaro, koda nawa za ta kashe, don tabbatar da zaman lafiya ya dawo jihar Imo gaba daya.

Gwamna Uzodimma ya kuma yi alƙawarin ziyartar Al'ummar Izombe don samun bayanai na farko na abin da ya faru da nufin kafa Kwamitin Bincike da zai duba musabbabin abinda ya faru.

‘Yan bindiga sun yi wa ‘yan sanda kwanton bauna, sun yi awon gaba da bindiga

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ake zargin' yan kungiyar asiri ne sun kai hari kan tawagar 'yan sanda da ke sintiri a kan hanyar Kolo zuwa Ogbia a karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani sifeton 'yan sanda ya samu rauni a harin yayin da aka kwace bindigarsa.

A cewar wata majiya daga yankin Kolo, lamarin ya faru ne mintuna kadan kafin tsakar dare a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An kama tsohon hadimin gwamna kan yada labaran karya, ya yanke jiki ya fadi a wajen gurfanar da shi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng