Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake sako dalibai 5 na makarantar Baptist, Kaduna

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake sako dalibai 5 na makarantar Baptist, Kaduna

  • 'Yan bindiga a jihar Kaduna sun sake sako dalibai biyar na makarantar Baptist Bethel da ke Kaduna
  • Rabaren Israel Adelani Akanji, ya tabbatar da sakin daliban 5 da aka yi tare da mai kula da su guda daya
  • A watan Yuli, miyagun sun sace dalibai 121 daga makarantar da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna

Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun sake sako karin dalibai biyar na makarantar Bethel Baptist da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Rabaren Israel Adelani Akanji, shugaban Nigerian Baptist Convention ya tabbatar da sakin daliban da aka yi a daren Juma'a.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake sako dalibai 5 na makarantar Baptist, Kaduna
Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sake sako dalibai 5 na makarantar Baptist, Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Godiya ta tabbata ga Ubangiji. Biyar daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist da mai kula da su 1 an sako su da yammacin nan, 8 Oktoba."

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

“Muna godiya ga Ubangiji kuma mun yarda cewa sauran daliban hudu za a sako su. Muna godiya da addu'o'in ku da goyon bayan ku," takardar tace.

Miyagun da suka kai farmakin sun yi awon gaba da dalibai 121 daga dakunan kwanansu kuma suka bukaci N500,000 a matsayin kudin fansan kowanne dalibi.

Tun daga nan, 'yan bindigan sun cigaba da sakin daliban kashi-kashi. A kashin farko an sako dalibai 28 a ranar 25 Yuli bayan iyayensu sun biya wasu kudin da basu bayyana ba.

Biyu daga cikin daliban sun tsero daga hannun 'yan bindigan yayin da suka sako daya sakamakon rashin lafiyan da ya ke fama da ita, Daily Trust ta ruwaito.

A ranar 26 ga watan Yuli, 3 daga cikin daliban sun sake tserowa daga hannun wadanda suka sace su.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'an ta sun ceto mutum shida da aka sace a kan babbar hanyar Barde zuwa Keffi da ke karamar hukumar Kafanchan ta jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis a garin Kaduna.

Jalige ya ce a ranar 5 ga watan Oktoba, jami'an 'yan sanda sun samu rahoton garkuwa da mutane da aka yi ranar hudu ga wata wurin karfe shida da rabi kan titin Barde zuwa Keffi, "cike da hankali tare da salo aka bibiye su tare da kai wa ga 'yan fashin dajin"

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel