Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su

Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su

  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kaduna sun ceci mutum shida da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
  • Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce sun kai dauki ne bayan sun samu labarin sace matafiya da aka yi
  • 'Yan sandan sun bi babbar hanyar Barde zuwa Keffi da ke karamar hukumar Kafanchan inda suka yi artabu da miyagun

Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce jami'an ta sun ceto mutum shida da aka sace a kan babbar hanyar Barde zuwa Keffi da ke karamar hukumar Kafanchan ta jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis a garin Kaduna.

Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su
Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC
Jalige ya ce a ranar 5 ga watan Oktoba, jami'an 'yan sanda sun samu rahoton garkuwa da mutane da aka yi ranar hudu ga wata wurin karfe shida da rabi kan titin Barde zuwa Keffi, "cike da hankali tare da salo aka bibiye su tare da kai wa ga 'yan fashin dajin"

Read also

Sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya yayin da take kara murmurewa

Ya ce jami'an sun yi artabu da masu garkuwa da mutanen, lamarin da yasa suka bar wadanda suka sace tare da neman mafaka a cikin dajin duk da raunikan da suka ji.

Ya ce cike da nasara suka ceto shida daga cikin wadanda aka sacen ba tare da sun samu rauni ba. Jalige ya ce tuni aka kwaso wadanda aka sacen kuma aka mika su ga 'yan uwansu, Daily Nigerian ta wallafa.

"An cigaba da tsananta wa tare da bazama neman 'yan bindigan da suka tsere," yace.

Kakakin rundunar 'yan sanda tare da hadin guiwar jami'an rundunar Operation Puff Adder II a ranar 2 ga watan Oktoba bayan samun bayanan sirri sun shiga dajin Yadi da ke yankin Fatika a karamar hukumar Giwa kuma sun yi artabu da 'yan bindigan.

Read also

Kano: Dalibar jami'ar Bayero ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

A wani labari na daban, Sakina Bello dalibar jami'ar Bayero ce da ke jihar Kano wacce ta ke aji uku na karatun ilimin tsirrai. Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar yayin da ta ke hanya tsakanin Janbulo da yankin Rijiyar Zaki ta jihar Kano a tsakiyar birnin Dabo.

Majiyoyi daga 'yan uwanta sun tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Nigerian inda suka ce an sace ta wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata yayin da ta ke cikin Keke Napep a hanyarta ta zuwa gida.

Zuwa safiyar Laraba, wadanda suka sace ta sun kira inda suka bukaci kudin fansa har naira miliyan Dari. Mai magana da yawun rundunar 'yan Sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce 'yan sanda sun samu rahoton batan Sakina wurin karfe 3 na yammacin Talata kuma a take suka fara bincike.

Read also

'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan binidiga man fetur

Source: Legit.ng

Online view pixel