Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

  • Zakakuran sojojin Najeriya sun sheke miyagu 3 da ake zargin 'yan awaren IPOB ne a jihar Enugu
  • Kamar yadda mai magana da yawun rundunar yace, miyagun sun kai wa 'yan sanda farmaki ne
  • Lamarin ya faru a babbar hanyar Okija zuwa Onitsha kuma soja daya ya rasa ransa yayin artabun

Enugu - Dakarun sashi na 5 na atisayen Golden Dawn da aka tura Enugu sun sheke mutum 3 da ake zargin 'yan awaren kudu ne da aka fi sani da IPOB, wadanda suka kai wa 'yan sanda farmaki kan babbar hanyar Okija zuwa Onitsha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar da kakakin dakarun sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar tace, zakakuran sojin sun yi artabu da miyagun kuma suka fi karfinsu, lamarin da yasa suka arce.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekaru 70 da wasu 2 dauke da makamai

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3
Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Dakarun sojin ba su kakkauta ba suka bi su tare da cigaba da zuba musu ruwan wuta. Uku daga cikin 'yan bindigan da ke tuka motoci biyu kirar Hilux da Hummer bus ne suka bakunci lahira yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika.
“Dakarun sojin sun samo mota daya da babura biyu yayin da suke duba dukkan yankin da 'yan ta'addan suka nufa.
“Cike da alhini, soja daya ya rasa ran sa a yayin da ya ke bai wa kasar sa kariya," Birgediya Janar Nwachukwu ya ce.

Shugaban dakarun sojin kasa ya jinjina wa sojojin kan wannan nasarar tare da kira garesu da su cigaba da tsanantawa tare da matsawa duk 'yan ta'addan da ke yankin.

COAS ya jajanta tare da mika ta'aziyyarsa ga iyalan zakakurin sojan da ya rasa ransa tare da yi masa fatan rahama, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Gbajabiamila da 'yan siyasa 58 da suka kashe miliyoyi wurin ziyartar Tinubu

A wani labari na daban, a kalla jiga-jigan 'yan siyasa 58 tare da wadanda ke rike da ofisoshin siyasa a kasar nan suka kashe miliyoyin naira wurin kai wa jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Boka Tinubu ziyara a London, Daily Trust ta ruwaito.

Tinubu jigon jam'iyya mai mulki ne wanda ya kwashe watanni uku a London ya na jinya. Makusancin tsohon gwamnan jihar Legas ya ce an yi masa aiki a guiwa kuma a halin yanzu likitocin kashi ne ke kula da shi.

Tun ranar 12 ga watan Augusta, yayin da shugaban kasa Muhammadu Burai ya ziyarcesa a London, yaransa na siyasa, masoyansa da magoya bayansu suka mayar da gidan tamkar filin arfa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel