Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

  • 'Yan haramtacciyar kungiyar nan ta sa-kai sun kashe akalla mutum 11 a kasuwar kauyen Mammande da ke Karamar Hukumar Gwadabawa a Jihar Sokoto
  • Cikin mutanen da aka kashe har da wani limami a garin Salame da ya je siyayya a kauyen na Mammade
  • ’Yan sa kan sun yi wa kasuwar dirar mikiya ne dab da la’asar, a lokacin da kasuwar ta cika makil sannan suka aiwatar da ta'asar

Wasu miyagu da ake zatton 'yan haramtaciyyar kungiyar sa-kai ne a jihar Sokoto, sun halaka mutane 11, ciki har da wani Limami, a kauyen Mamande da ke karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.

Jaridar Daily trust ta rahoto cewa wadanda abin ya rutsa da su sun mutu nan take yayin da karamar hukumar ta kai wasu mutane hudu da samu raunin harbin bindiga zuwa asibiti domin yi musu magani.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekaru 70 da wasu 2 dauke da makamai

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto
Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto Hoto: Spread.ng
Asali: UGC

Limamin wanda aka bayyana sunansa da Malam Aliyu an ce yana jagorantar Sallah a daya daga cikin Masallatan na yau da kullum a Salame.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rahoto, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Alhamis.

An tattar cewa wadanda abin ya rutsa da su sun fito ne daga garuruwan Fulani daban-daban da ke kusa da yankin don siyan abinci da sauran kayayyaki a kasuwar Mamande na mako-mako.

Miyagun sun shiga kasuwar ne daga Karamar Hukumar Goronyo, sannan suka kaddamar da hari kan wadanda abin ya cika da suke zargi da taimakawa 'yan fashi.

Wani dan uwan limamin, Abdullahi Riskuwa, ya ce an kashe dan uwansa ba tare da hujja ba saboda bai taba aikata wani laifi ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 21 sakamakon bude wuta da suka yi a cikin kasuwa a Sokoto

Ya ce:

"Yana da cikakkiyar ilimin addini kuma yana jagorantar sallah a daya daga cikin masallatan mu a garin Salame.
"Laifinsa kawai shine ya kasance dan kabilar Fulani ne."

A cewar Riskuwa, Imam Aliyu ya je kasuwa ne kawai don sayo kaya lokacin da aka kashe shi.

Daga cikin wadanda aka kashe a kasuwar, ya ce yara ne kuma Yan Sakai din sun tafi da dabbobinsu.

Ya yi kira ga gwamnati da ta binciki lamarin da nufin gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi.

Shugaban kungiyar Miyeti Allah na jihar, ba a iya jin ta bakinsa ba saboda layin wayarsa bai isa ba lokacin da aka yi kokarin magana da shi.

A halin da ake ciki, Shugaban Karamar Hukumar Gwadabawa, Aminu Aya, ya tabbatar da harin, yana mai cewa Yan Sakai ba daga Gwadabawa suke ba.

A cewarsa, an ajiye mamatan a dakin ajiye gawa na asibitin kwararru, Sokoto, kuma wasu daga cikin danginsu sun je wurin don kwaso gawarwakinsu.

Kara karanta wannan

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Sai dai ya ce, an dawo da zaman lafiya a yankin.

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A gefe guda, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda su ka halaka mutane 19 sannan su ka yi garkuwa da mutane 21 a daren da su ka kai farmaki garin Gatawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel