Wasanni: Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle

Wasanni: Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle

  • Kasar Saudiyya ta samu nasarar cimma burin saye kungiyar kwallon kafan Firmiya ta Newcastle
  • Rahotanni sun bayyana cewa, yanzu Newcastle za ta zama daya daga cikin kungiyoyin da suka fi kudi a duniya
  • Tuni an kammala duk wasu sanya hannu da ka'idojin doka da sayen kungiyar ya tanada

Saudiyya - Kungiyar kwallon kafa mai buga Firimiya a kasar Ingila, Newcastle United ta koma hannun wata kungiyar da Saudiyya ke marawa baya, Al-Jazeera ta ruwaito.

Kungiyar ta Newcastle United ta amince da cinikin bayan wasu takardun doka sun tabbatar da cewa kasar ba za ta yi tasiri kan harkoki ko iko da kungiyar ba.

Kasar Saudiyya ta sayi kungiyar kwallon kafa ta Newcastle
Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle | Hoto: forbes.com
Asali: UGC

A cewar sanarwar Firimiya:

"Kungiyar Gasar Firimiya, Newcastle United Football Club da St James Holdings Limited sun warware takaddamar da ake yi kan karbe kungiyar daga hannun PIF, PCP Capital Partners da RB Sports & Media"

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, duk da cewa 80% cikin 100% na kudaden cinikin fam miliyan 300 da aka kulla kan kungiyar ya zo ne daga asusun ajiya na zuba hanayen jarin kasar, hakan ba zai shafi gudanar da kungiyar ba.

A yanzu dai mallakar kungiyar a hannun Saudiyya ya tsallake duk wani cike-ciken takardu tsakanin kungiyar ta firimiya da shugabanninta.

Kungiyar na shirin zama daya daga cikin kungiyoyin da suka fi kowa kudi a duniya, inda dukiyar su za ta ninka ta masu Man City ninki goma kuma kusan ta ninka ta Paris Saint-Germain sau 50, inji rahoton Daily Mail.

A halin da ake ciki, 'yan wasan Newcastle da ma'aikata da koci sun motsa jiki a ranar Alhamis yayin da labarin sabon sauyin ke gabatowa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Kocin Super Eagles, Gernot Rohr ya na bin albashin watanni 8, bashin N150m ya taru a kan NFF

A Najeriya kuwa, Kocin tawagar ‘yan wasan kwallon kafan Super Eagles, Gernot Rohr yana bin hukumar kwallon kafan Najeriya, NFF albashin watanni takwas.

PUNCH Sports Extra ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, 2021 cewa hukumar NFF tayi watanni takwas ba ta biya Gernot Rohr kudin shi ba.

Kocin kasar wajen da ya taimaka wajen horas da ‘yan Super Eagles zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika na 2022 ya dauki lokaci bai karbi albashinsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel