Kocin Super Eagles, Gernot Rohr ya na bin albashin watanni 8, bashin N150m ya taru a kan NFF

Kocin Super Eagles, Gernot Rohr ya na bin albashin watanni 8, bashin N150m ya taru a kan NFF

Gernot Rohr yana bin hukumar kwallon kafan Najeriya albashin watanni takwas

Tun a 2020, duk wata NFF tana biyan Gernot Rohr da ma’aikatansa Dala $45, 000

Ana sa ran ba da dade wa ba za a biya Baturen kocin da ‘yan tawagarsa kudinsu

Abuja - Kocin tawagar ‘yan wasan kwallon kafan Super Eagles, Gernot Rohr yana bin hukumar kwallon kafan Najeriya, NFF albashin watanni takwas.

PUNCH Sports Extra ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, 2021 cewa hukumar NFF tayi watanni takwas ba ta biya Gernot Rohr kudin shi ba.

Kocin kasar wajen da ya taimaka wajen horas da ‘yan Super Eagles zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika na 2022 ya dauki lokaci bai karbi albashinsa ba.

Rahoton yace rabon da NFF ta biya Gernot Rohr albashi tun watan Fubrairun shekarar nan.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nawa ake biyan kocin a wata?

Abin da ake biyan Rohr a wata shi ne $45,000 a duk wata (kusan Naira miliyan 20 a kudin Najeriya) tun da ya sa hannu a sabon kwantiraginsa a 2020.

Gernot Rohr
Babban Kocin Super Eagles, Gernot Rohr Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Daga cikin wadannan kudi ne Rohr yake biyan masu yi masa bibiyar ‘yan wasa masu taso wa da masu horas masa da ‘yan wasa, da masu nazarin bidiyo.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai za a biya Rohr albashin da yake bi bashi da kudin gida na Naira, a madadin Dalar Amurkar da ya saba karba.

Haka zalika hukumar NFF ta kasa ta gagara biyan ‘yan tawagar Rohr alawus dinsu na nasarar da suka samu a wasan Super Eagles da kasar Cape Verde.

Abin da hukumar NFF take cewa

Wani jami’in hukumar kwallon kafa na kasar ya bayyana cewa za a biya masu horas da ‘yan wasan duk alawus dinsu bayan wasan Central African Republic.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 30 ana bincike, an samu rigakafin ciwon zazzabin cizon sauro, Malariya

“Ba na so in yi magana kan wannan. Akwai wasan da ke gabanmu, kuma muna sa rai za a shawo kan matsalar bayan wasan kasar against Central African Republic.”

Kocin Barcelona yana ganin ta kan shi

A kwanakin baya aka ji cewa ana rade-radin za a sallami Ronald Koeman daga aikinsa a Barcelona, ganin yadda kulob din bai samun nasara a wasanni.

Daga cikin wadanda ake gani za su iya gadon kujerarsa akwai Xavi Hernandez. Tsohon 'dan wasan tsakiyan zai yi sha'awar dawo wa kungiyar da ya bari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel