Dalilin da yasa muka rushe gidan dan majalisar tarayya a jihar mu, Gwamnan Arewa

Dalilin da yasa muka rushe gidan dan majalisar tarayya a jihar mu, Gwamnan Arewa

  • Gwamnatin jihar Bauchi, ta bayyana cewa ta ɗauki matakin rushe gidan ɗan majalisar tarayya ne saboda ya tara yan daba a ciki
  • Mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, yace ba'a bi ta hanyar da ya dace ba wajen mallakar filin wurin
  • Ya tabbatar da cewa gwamnatin Bauchi ba zata bar duk wani abu da ya zama barazana ne ga tsaron al'umma ba

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa ta rushe gidan ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar garin Bauchi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Gwamnatin tace ta ɗauki wannan matakin ne bayan samun rahoton sirri cewa ɗan majalisar ya ɓoye yan daba a gidan, wanda hakan barazana ce ga tsaron yankin.

Mai baiwa gwamna shawara kan yaɗa labarai, Kwamaret Mukhtar Gidado, shine ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ya gudana a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Nasarorin Gwamnati da Twitter Kan Hana Amfani da Dandalin a Najeriya, Makusancin Buhari

Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed
Dalilin da yasa muka rushe gidan dan majalisar tarayya a jihar mu, Gwamnan Arewa Hoto: arise.tv
Asali: UGC

Ta ya ɗan majalisar ya mallaki gidan?

Gidado ya bayyana cewa gidan wanda ke a lamba 7, hanyar Buba Yero, GRA, Bauchi, babu wanda keda hurumin siyar da shi ba tare da amincewar gwamna ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, Abubakar Tatari, ya yi fatali da dukkan wasu matakai da aka shinfiɗa, kuma ya mallakawa kansa filin ta hanyar amfani da wani mai suna, Muhammed Kabir.

A cewarsa, daga bisani kuma aka siyarwa dan majalisa, Honorabul Yakubu Shehu Abdullahi, kan kudi naira miliyan N9m.

Kwamaret Gidado ya bayyana cewa lokacin da jami'an gwamnati suka je rushe ginin, yan daban da ɗan majalisar ya aje, sun buɗe wuta kan jami'an tsaro.

Meya faru lokacin rushe ginin gidan?

A jawabinsa, Gidado yace:

"Tawagar gwamnatin jiha, bisa jagoranci sakataren gwamnati, sun ziyarci wurin domin tabbatar da abinda ke faruwa."

Kara karanta wannan

Zamu dandana musu zafin da mutane ke ji, Gwamna ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindiga

"Da zuwansu wasu yan daba suka farmake su, wanda hakan yasa suka bar wurin don gudun abun ya munana."
"Bayan haka, gwamnatin jiha ta sake shigar da ƙorafi kan taruwar yan daba ɗauke da makamai a wurin ginin gida dake bayan gidan gwamnati."

Gidado ya ƙara da cewa gwamnatin gwamna Bala Muhammed, tana aiki ba dare ba rana domin tabbatar da kare rayuwar al'umma da dukiyoyinsu.

A wani labarin kuma Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

An shiga tashin hankali a Awka, babban birnin jihar Anambra, biyo bayan hallaka mutum 3 da yan bindiga suka yi a birnin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Maharan sum bindige mutanen ne a kusa da kasuwa dake Ifite yayin da aka kashe mutum ɗaya a bayan asibitin koyarwa na Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, Amaku, ƙaramar hukumar Awka ta kudu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel