Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

  • Mutane sun shiga tashin hankali da fargaba yayin da wasu miyagun yan bindiga suka hallaka mutum uku a jihar Anambra
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutanen ne a wuri biyu kuma cikin minti 15 na yammacin ranar Talata
  • Har zuwa yanzun hukumar yan sandan jihar ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba, amma wani jami'i ya tabbatar

Anambra - An shiga tashin hankali a Awka, babban birnin jihar Anambra, biyo bayan hallaka mutum 3 da yan bindiga suka yi a birnin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Maharan sum bindige mutanen ne a kusa da kasuwa dake Ifite yayin da aka kashe mutum ɗaya a bayan asibitin koyarwa na Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, Amaku, ƙaramar hukumar Awka ta kudu.

Wani shaidan gani da ido, ya faɗawa The Nation cewa lamarin biyu sun faru ne a tsakanin ƙarfe 4:15 - 4:30 na yammacin ranar Talata.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina

Jihar Anambra
Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Bisa faruwar hakane mazauna garin Awka suka shiga cikin tashin hankali domin sun jima basu ga kisa irin wannan ba a yan kwanakin nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya kawo faruwar lamarin?

Tun a baya an samu saukin yawan kashe-kashe bayan wasu mutanen yankin sun gayyaci yan tawagar da ake kira 'Bakassi boys' domin magance matsalar.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa lamarin na Ifite ya faru ne bayan wasu sanannun masu faɗa a ji na yankin sun ki amincewa jami'an tsaro su shiga lamarin.

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, yace ba shi da masaniya a kan faruwar kisan.

Amma wani babban jami'i a hukumar yan sanda, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya tabbatar da faruwar Lamarin.

A wani labarin kuma Wajibi jam'iyyar PDP ta yi abu daya matukar tana son fatattakar APC a 2023, Shugaban Matasa

Kara karanta wannan

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Shugaban matasan PDP, Aliyu Bello, ya gargaɗi jam'iyyarsa kan kada ta yi kuskuren kai tikitin takarar shugaban ƙasa yanki ɗaya

A cewarsa, kamata ya yi a bar kofa a buɗe ga duk wanda ke sha'awar tsayawa takara daga kowane yanki, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel