Zamu dandana musu zafin da mutane ke ji, Gwamna ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindiga

Zamu dandana musu zafin da mutane ke ji, Gwamna ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindiga

  • Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cewa ba zai sake amincewa wasu tsirarun mutane su cigaba da kashe mutane a jiharsa ba
  • Umahi yace idan ya sake jin an tada zaune tsaye ko an kashe wasu, to zai kama iyaye, sarakuna da shugabannin yanki da laifi
  • A cewar gwamnan, kowa ya cigaba da fita harkokinsa na yau da kullum ranar Litinin, a barwa gwamnati sauran

Ebonyi - Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, ya bayyana cewa zai kame iyayen duk wanda aka gano yana da hannu a kashe-kashen dake faruwa kwanan nan a jihar.

The cable ta ruwaito cewa gwamnan ya faɗi haka ne bayan sa hannu a kwantiragin gina hanyar Abakaliki ring, wanda ya gudana a ofishinsa.

Umahi ya ƙara da cewa waɗannan hare-haren da al'umma ke fama da shi ya isa haka, gwamnati ba zata cigaba da lamurta ba.

Kara karanta wannan

Dalilin Na Yasa Muka Nemi Afuwar Yan Najeriya Kan Yadda Muka Gudanar Da Mulki, Aisha Buhari

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi
Zamu dandana musu zafin da mutane ke ji, Gwamna ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindiga Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewar wata sanarwa da kakakin gwamnan, Francis Nwaze, ya fitar, Gwamnan yace idan masu aikata wannan kashe-kashen aiki suke bukata, gwamnatin jiha zata samar musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa ya kamata a ɗorawa alhakin matsalar?

Bugu da ƙari, gwamnan ya yi gargaɗin cewa idan ya sake jin an tada yamutsi a jihar, sarakunan gargajiya da shugabannin yanki, su zai kama da laifi.

Dailytrust ta ruwaito Umahi yace:

"Bazan sake yarda da kashe-kashe ko ƙona gidaje a jihata ba, idan matsalar miyagun itace rashin aiki, to a kawo mun su, zan samar musu aiki."
"Amma idan suka ƙi amsar wannan tayin, kuma kuka gaza kawo mun sunayensu, to ku abun zai shafa."
"Bayanai kaɗai nake bukata, idan sun amince da wannan tayin, ba zamu kama kowa ba. Zan ɗauke su aiki kuma a canza musu tunani, amma babu wanda zai sake kashe wani."

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Wane mataki Umahi zai ɗauka kan dokar zaman gida?

Game da dokar IPOB ta zaman gida duk ranar Litinin, Umahi ya yi kira ga al'umma su fita harkokin kasuwancinsu kamar yadda suka saba, su barwa gwamnati sauran.

Yace:

"Jami'an tsaro zasu fita sintiri ko ina, saboda kunsan yaran nan kuma kunsan iyayensu. Idan aka sake aikata kisa, to zamu fuskanci iyayensu ne."
"Zamu ɗanɗana musu irin ciwon da ake ji, wajen zubar da jinin al'ummar da ba su ji ba basu gani ba."

A wani labarin kuma Yan sanda sun damƙe gungun masu garkuwa dake aiki a tashoshin Mota a Birnin Kano

Kakakin rundunar yan sanda ta ƙasa, Frank Mba, ya bayyana cewa jami'an sun kwato manyan makamai daga hannun mutanen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga hannun, ya bayyana cewa yana ɗakko fasinja daga tashar mota domin garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262