Nasarorin Gwamnati da Twitter Kan Hanin Amfani da Dandalin a Najeriya, Makusancin Buhari

Nasarorin Gwamnati da Twitter Kan Hanin Amfani da Dandalin a Najeriya, Makusancin Buhari

  • Mai taimakawa shugaba Buhari ta ɓangaren watsa labarai, Ogunlesi, yace kowane ɓangare ya yi nasara kan hana amfani da Tuwita
  • Yace tattaunawar gwamnatin tarayya da kamfanin tuwita na gab da kawo wa ƙarshe, domin kowa ya fahimci ɗaya ɓangaren
  • Gwamnatin Buhari ta hana amfanin da shafin sada zumunta na Tuwita ne tun bayan goge rubutun shugaba Buhari

Abuja - Mai taimakawa shugaban ƙasa Buhari na musamman, Tolu Ogunlesi, yace hana amfani da shafin Tuwita a Najeriya nasara ce ga kowane ɓangare, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ogunlesi, wanda yana ɗaya daga cikin tawagar gwamnatin Najeriya dake tattaunawa da kamfanin tuwita domin warware dukkan matsaloli.

Hana Tuwita a Najeriya
Nasarorin Gwamnati da Twitter Kan Hanin Amfani da Dandalin a Najeriya, Makusancin Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya yi wannan furuci ne a wata hirar kai tsaye da CNN, yayin da yake amsa tambayoyi kan goyon bayan hana amfani da tuwita.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

Yace:

"A tunanina wannan hanin nasara ce ga gwamnatin Najeriya kuma nasara ce ga kamfanin tuwita. Wannan shine abinda na fahimta daga tattaunawar da ake yi."

Yaushe za'a cimma matsaya?

A cewar Ogunlesi, ɓangarorin biyu na cigaba da fahimtar juna a tattaunawar kuma ba da jimawa ba za'a cimma matsaya.

"Muna gab da warware komai kuma kowane ɓangare ya amfana daga sauraron bayanan ɗaya bangaren."

A rahoton da NetBlocks ya fitar tun bayan hana amfani da Tuwita, Gwsmnatin Najeriya ta yi asarar kuɗaɗen shiga kimanin biliyan N272bn, kamar yadda The cable ta ruwaito.

Shin hana tuwita yana da alaƙa da goge rubutun shugaba Buhari?

Sai dai, Ogunlesi ya ƙi bada amsa kai tsaye kan cewa hana amfani da dandalin sada zumuntan ya samo asali ne daga goge rubutun shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa a 2023

A wani labarin kuma Wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023, Tsohon Minista ya magantu

Tsohon minista a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya bayyana cewa jigon APC, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023.

Ogunlewe ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa za'a ƙaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu reshen mahaifarsa, jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262