Korona ta yi ajalin babban lauyan Najeriya duk da cewa ya yi allurar riga-kafi

Korona ta yi ajalin babban lauyan Najeriya duk da cewa ya yi allurar riga-kafi

  • Kwararren lauyan Najeriya, Oladipupo Williams ya rasa ran sa sakamakon cutar Covid-19 duk da anyi masa riga-kafin cutar
  • A wata wallafa wacce dan sa, Kunle ya yi a shafin sa na Facebook, ya ce mahaifin sa ya rasu a ranar Lahadi
  • Kamar yadda ya bayyana, an yi wa mahaifin na sa riga-kafin da allurar Oxford AstraZeneca kafin rai ya yi halin sa

Jihar Legas - Wani babban lauyan Najeriya, Oladipupo Oladipupo, SAN, ya rasa ransa a ranar Lahadi sakamakon cutar Covid-19 duk da anyi ma sa riga kafin cutar da allurar Oxford Astrazeneca.

Oladipupo ne dan alkali marigayi Chief Fredrick Rotimi Williams.

Korona ta yi ajalin babban lauyan Najeriya duk da cewa ya yi allurar riga-kafi
Oladipupo Williams, SAN. Hoto: The Punch
Source: Facebook

Read also

Da dumi-dumi: Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, kanin Mama Taraba, rasuwa

A wata wallafa wacce dan Oladipupo, Kunle ya yi, ya bayyana cewa mahaifin sa ya rasa ran sa a ranar Lahadi a wani asibitin kudi dake jihar Legas.

A cewar sa ya rasu ne a wani asibiti a Legas

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya yi wallafar ne kamar haka:

“Mahaifi na ya amsa kiran Ubangijin sa da safiyar yau sakamakon cutar COVID-19 duk da anyi ma sa riga-kafin cutar har sau biyu da allurar Oxford AstraZeneca.”

Oladipupo ya zama lauya tun shekaru 48 da su ka gabata kuma ya zama babban lauya, SAN a shekarar 1995.

Babban lauya ne shi a majalisar lauyoyi ta Chief Ladi Rotimi-Williams, wata majalisar lauyoyi dake jihar Legas.

Babban lauyan ya na daya daga cikin manyan lauyoyin dake kasar nan masu gogewa da kwarewa a harkar shari’a.

Wani farfesa ya bayyana cewa duk da riga-kafin mutum na iya fama da cutar

Read also

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

A wata tattaunawa da The Punch ta yi da Oyewale Tomori, wanda farfesa ne a Virology, a ranar Lahadi ya bayyana wa wakilin Punch, cewa ko da anyi wa mutum riga-kafin COVID-19 zai iya mutuwa sanadin cutar.

Kamar yadda ya ce:

“Don anyi wa mutum riga-kafin cutar ba yana nufin ba zai taba kamuwa da cutar bane. Bisa dalilai masu yawa kowa akwai yadda allurar za ta yi aiki a jikin sa. Hakan zai sa riga-kafin ba lallai ta yi aiki a jikin mutum dari bisa dari ba.”

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Read also

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Source: Legit

Online view pixel