Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

  • Dr Penking ya bayyana yadda mutane suke ta barazanar halaka shi sakamakon bude wani wurin gwajin DNA da ya yi a anguwar su
  • Kamar yadda ya bayyana, zai bude wurin gwajin ne a watan Oktoba kuma bisa rahusa wanda hakan bai yi wa mutane da dama dadi ba
  • Sun yarda da cewa ganin rahusar zai sa maza su yi tururuwar gwaji don gane gaskiyar batu idan su ne iyayen yaran su na hakika

Legas - Wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya bayan buɗe wurin gwajin DNA
Likitan Najeriya da ya bude wurin gwajin DNA ya kuma yi rangwamen kashi 70 cikin dari. Hoto: Dr PenKing
Asali: Facebook

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Kamar yadda yayi wallafar:

“Zamu bude sabon wurin gwajin DNA a ranar 18 ga watan Oktoba kuma za a samar da rahusar kaso 75 bisa dari ga gwajin tabbatar da mahaifin yaro na gaskiya na wata daya. Na sa hannu da MD yau. Mutane da dama a Najeriya ba za su san ya anko iri daya ba a wannan watan Disamban.
“Tun daga arewacin Ireland, wani likita mai murabus ya gano yadda mata su ke damfarar maza da yaran da ba nasu ba a Najeriya kuma ya yanke shawarar zuwa ya cece su a Lekki. Biloniyoyin Najeriya da dama ba su iya amfani da dama ba a kasar nan.”

Kara karanta wannan

Hoton tsohon rasit da ke nuna an siya buhu 40 na siminti kan N1520 ya janyo cece-kuce

Bayan sa’o’i kadan da wallafar mutane su ka fara ja ma sa kunne

Bayan sa’o’i kadan da wannan wallafar, Dr Penking ya koma Twitter inda ya bayyana yadda wasu mutane suka fara ja ma sa kunne akan tallata wurin gwajin DNA din ko kuma ya rasa ran sa.

Kamar yadda ya wallafa bisa ruwayar Pulse Nigeria:

“Yanzu haka mutane sun fara tururuwar yin barazana ga rayuwa ta kan cewa in dakata daga tallata wurin gwajin DNA har da sanya rahusar kaso 75 bisa dari da zan kaddamar a Lekki. Gaskiya damfarar da ake yi wa maza ana cusa mu su yaran da ba nasu ba ya yi yawan da baka tunani. Na san ana yi amma ban yi tunanin lamarin ya kai haka ba. Ikon Allah!
“Ko da wannan ne zai kasance wallafar karshe da zan yi, ina shawartar mazan Najeriya da su yi kokarin tabbatar da cewa yaran da suke kulawa da su yaran su ne na jini. Ko da ba ka da kudin yi, ka gwada yi wa yaron ka na farko.

Kara karanta wannan

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

“Kada ka bari wata ta cusa maka yaran da ba naka bane. Ba wai rashin yarda bane, sanin gaskiyar lamari ne. Maza da dama sun yarda da matan su amma idan su ka bincika ba yaran su na asali bane suke rikewa.
“Ka ceci kan ka daga asarar kudi. Ka tabbatar tun da wuri. Ko wanne uba ya kula da yaran sa ba na wani ba.”
“Ganin halin da muke ciki a Najeriya, zai fi dacewa ka tabbatar da ko da dan ka na farko ne idan kai ne asalin mahaifin sa ko akasin hakan.”

NAFDAC ta kama mutane 24 da ke sayar da maganin ƙarfin maza a Sokoto

A wani labarin daban, hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na kasa, NAFDAC, ta kama mutane 24 da ke talla da sayar da magungunan kara karfin maza na gargajiya mara rajista a garin Sokoto.

Shugaban hukumar na jihar Sokoto, Garba Adamu, ya bayyana cewa NAFDAC ta kama motocci shida da na'urar amsa kuwwa da ake amfani da su wurin sayar da jabun magunguna.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama mutumin da ke taimakawa masu garkuwa karɓar kuɗin fansa

Ya ce kayan da darajarsu ya kai Naira miliyan 2 an kwato su ne a kasuwanni da titunan birnin Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164