Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

  • EFCC tace an sace kimanin Naira biliyan 160 a asusun fanshon tsofaffin ma’aikata
  • Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa yace za su yaki masu taba kudin mutane
  • Bawa ya sha wannan alwashin wajen wani taro da aka gudanar jiya a garin Abuja

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya tace ta binciki badakalar kudin fansho, inda ake gano cewa an saci akalla Naira biliyan 157.

A ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2021, jaridar Punch ta rahoto darektan EFCC, Adulkarim Chukkol, yana bayani a kan kudin fanshon da wasu ke sata.

Malam Chukkol ya bayyana wannan a wajen wani taron da aka shirya a garin Abuja domin kara wa juna sani da nufin kauda satar kudin fansho a Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Kamar yadda jaridar Vanguard ta fitar da rahoto, shugaban EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin kawo karshen taba kudin fansho da ake yi.

“Mun yi bincike, kuma mun tattara satar biliyoyin kudin da ake yi a harkar fansho.”
“Baya ga kudin da ‘yan fansho suka rasa, sun yi asarar da ba za ta misaltu ba. Za su je suna yawo, suna rokon mutane domin su iya karbar kudin da suka tara.” - Abdulrasheed Bawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Hukumar EFCC
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa a Majalisa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abin kunya ne - Bawa

A jawabinsa, Abdulrasheed Bawa yace abin kunya ne a ce wadanda suka yi shekaru suna adana kudinsu, za su koma suna shan wahala bayan sun yi ritaya.

Shugaban EFCC ya koka a kan dokokin fansho da yadda ake mu’amala da dukiyar tsofaffin ma’aikata.

Rahoton yace makasudin shirya taron shi ne domin a samar da tsarin fansho na gaskiya da adalci, ta yadda zai yi wahala a iya dauke kudin masu ritaya.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

A jawabin Boss Mustapha wanda shi ne babban bako a wajen taron, ya bayyana irin kokarin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi wajen hana satar fansho.

Doyin Okupe zai ceci talakan Najeriya?

Dazu aka ji Tsohon Mai magana da yawun Shugaban kasa, Doyin Okupe zai tsaya takarar shugaban kasa. Okupe yace zai nemi takarar ne domin Talaka.

Dr. Doyin Okupe yace Talaka zai ji dadi idan ya yi mulki, sannan ya yi alkawarin samar da 30000MW wanda hakan zai bunkasa harkar lantarki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel