Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

  • Vandu Weida mai shekaru 29 da yara 3 ya halaka kan sa bayan ya sha guba a ranar Talata
  • Hakan ya biyo bayan wani rikici wanda ya janyo tashin hankali tsakanin sa da matar sa
  • Rikicin ya auku ne a Mildu Central dake karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa

Jihar Adamawa -Wani magidanci mai suna Vandu Weida, mai shekaru 29 ya riga mu gidan gaskiya sakamakon gubar da ya sha.

Lamarin ya faru ne a Mildu Central, a karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa ranar Talata.

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa
Taswirar Jihar Adamawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Vandu, mai yara 3 ya samu hayaniya ne tsakanin sa da matar sa wanda har ya koma gagarumin fada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Punch ta ruwaito, wani ganau ya ce yayin fadan, Weida ya bayyana wa matar sa cewa ya gaji da ita da duniyar ma baki daya don haka ya gwammaci ya mutu ya bar ta da yaran.

Kara karanta wannan

Yobe: Mata mai juna biyu ta haɗa baki da wasu maza 2 wurin garkuwa da kanta

Bayan fadan, mutumin ya kasa jurewa hakan ya sa ya sha guba daga baya a ka gan shi a kasa yana numfashi da kyar.

Likitoci sun tabbatar gubar ta lalata ma sa hanji

Anyi gaggwar wucewa da shi babban asibitin Mubi inda aka tabbatar da cewa gubar da ya sha ta lalata ma sa hanji.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje ya ce bai san komai akan lamarin ba amma ya yi alkawarin bincike a kan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Madagali.

Har lokacin cike rahoto be nemi wakilin The Punch ba.

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kara karanta wannan

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164