Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya gana da wani Gwamna da kuma mambobin Darikar Tijjaniya

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya gana da wani Gwamna da kuma mambobin Darikar Tijjaniya

  • Khalifan Tijjanaiya a Najeriya kuma tsohon sarkin Kano, Muhammdu Sanusi II, ya kai ziyara ga mambobin darikarsa na Patakwal
  • Tsohon sarkin yace Ɗarikar Tijjaniya bata goyon bayan tashin hankali da ayyukan ta'addanci, kungiyace ta zaman lafiya
  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga yan Najeriya su haɗa kansu domin ceto ƙasa daga halin da take ciki

Rivers - A ƙarshen makon nan, tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ziyarci mambobin ɗarikar Tijjaniyya a Patakwal, jihar Rivers, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sanusi II ya kai ziyara ga gwamnan jihar, Nyesom Wike, a fadar gwamnatin jihar, kafin ganawarsa da mambobin Tijjaniya.

Tsohon sarkin ya bayyana cewa ya kawo ziyara ga yan ɗarikar Tijjaniya mazauna jihar Ribas ne domin shine jagoransu (Kalifa).

Read also

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

Tsohon sarki, Sanusi II
Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya gana da wani Gwamna da kuma mambobin Darikar Tijjaniya Hoto: hotpen.net
Source: UGC

Khalifa Sanusi ya tabbatar wa gwamna Wike cewa yan Tijjaniyya basa goyon bayan aikata ta'addanci, amma suna ƙaunar zaman lafiya, yan uwantaka, zaman tare, da cigaban ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan Tijjaniya masu son zaman lafiya ne - Sanusi

Sanusi ya ƙara da cewa ƙungiyar Tijjaniya, ƙungiya ce dake som zaman lafiya a koda yaushe, kuma baya goyon bayan masu aikata ta'addanci.

Khalifa yace:

"Wannan ziyarar ƙara sanin juna ne da kuma ganawa da shugabanni da mambobin Darikar Tijjaniya dake zaune a nan Patakwal."
"Ina godiya ga mai girama gwmana, sun bani labarin irin kyautatawar da kake musu kuma muna ganin yadda kake kokarin maida jihar Ribas kamar gida ga kowane ɗan Najeriya."
"Ina mai tabbatar maka da cewa ƙungiyar Tijjaniya, kungiya ce ta sufanci, kuma an santa da zaman lafiya."

Gwamna Wike ya yi kira a haɗa kai

Read also

Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 60 sun fito sun ce ba su goyon bayan a maidawa 'Yan Kudu mulki

A jawabinsa, Gwamna Wike ya yi kira ga yan Najeriya su haɗa kansu domin ceto Najeriya daga halin ƙaƙanikayi da ta tsinci kanta a ciki.

A cewar gwamnan tattalin arzikin Najeriya baya amfanar da komai ga yan ƙasa kuma a ganinsa tattalin arzikin ya gaza.

Wike ya ƙara da cewa talauci ba ruwansa da yare ko ƙabila saboda haka ya zama wajibi a haɗa kai domin haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

A wani labarin kuma Kamfanin sada zumunta Twitter ya yi martani kan kalaman shugaba Buhari na ranar samu yancin kai

Dandalin sada zumunta Twitter ya nuna jin daɗinsa bisa kalaman shugaba Buhari na ɗage hanin da aka masa idan ya cika sharuɗɗa.

A cikin jawabinsa na ranar yancin kai, Buhari yace gwamnati a shirye take ta ɗage hanin amfani da twitter da zaran an cimma matsaya.

Source: Legit.ng

Online view pixel