Kamfanin sada zumunta Twitter ya yi martani kan kalaman shugaba Buhari na ranar samu yancin kai
- Dandalin sada zumunta Twitter ya nuna jin daɗinsa bisa kalaman shugaba Buhari na ɗage hanin da aka masa idan ya cika sharuɗɗa
- A cikin jawabinsa na ranar yancin kai, Buhari yace gwamnati a shirye take ta ɗage hanin amfani da twitter da zaran an cimma matsaya
- Gwamnatin shugaba Buhari ta hana amfani da shafin Twitter ne a watan Yuni, bayan dandalin ya goge rubutun shuagaban ƙasa
Abuja - Kamfanin tuwita ya bayyana jin daɗinsa bisa kalaman shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na amincewa da ɗage hanin da aka masa idan ya cike wasu sharuɗɗa.
Kamfanin, wanda a halin yanzun baya aiki a Najeriya, yana fatan tattaunawa da FG yasa a bar shi ya cigaba da ayyukansa a Najeriya.
Kamfanin, mamallakin shafin sada zumunta na tuwita, ya faɗi haka ne ta bakin wani kakakinsa, wanda aka sakaya sunansa, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
A cewarsa, tattaunawar dake gudana tsakanin twitter da gwamnatin Najeriya tana da alfanu sosai kuma za'a cimma matsaya.
Yace:
"Tattaunawar mu da gwamnatin Najeriya tana da matuƙar muhimmanci, kuma za'a cimma matsaya domin dawo da ayyukan shafin twitter, muna fatan haka."
Wane kalamai Buhari ya yi kan Twitter?
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa matukar dandalin Twitter yacike wasu sharuɗɗa da gwamnati ta kafa, to za'a ɗage hanin da aka masa.
A cikin jawabin da ya yi ga yan Najeriya a ranar yanci, Buhari yace tawagar FG ta gana da Twitter kan batutuwa da dama.
Daga cikin abubuwan da suka tattauna, akwai biyan cikakken haraji, tsaro, da kuma warware wasu taƙaddama dake tsakani.
Gwamnatin Buhari ta dakatar da dandalin sada zumunta na Twitter ne a watan Yuni, biyo bayan goge rubutun shugaban ƙasa Buhari.
A wani labarin daban Gwarazan yan sanda sun ceto iyalan kakakin majalisa da wasu mutum 11 daga hannun miyagu
Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, ranar Asabar, ta sanar da ceto iyalan kakakin majalisar dokokin Zamfara da aka sace tun 5 ga watan Agusta, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, shine ya tabbatar da haka yayin da ya gabatar da waɗanda aka ceto gaban manema labarai a Gusau.
Asali: Legit.ng