Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 60 sun fito sun ce ba su goyon bayan a maidawa 'Yan Kudu mulki

Zaben 2023: Kungiyoyin Arewa 60 sun fito sun ce ba su goyon bayan a maidawa 'Yan Kudu mulki

  • Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya ta tsaida matsaya game da zaben 2023
  • CNG tace ba ta goyon bayan a ware wa Kudancin Najeriya tikitin shugaban kasa
  • Kakakin CNG, yace matsayar ta zo daya da ta dattawa da gwamnonin Arewa 19

Abuja - Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, ta nuna adawarta ga tsarin karba-karba da jam’iyyun siyasa suke kawo wa yayin da ake shirin zabe.

Mai magana da yawun bakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya bayyana cewa wannan tsaro ya saba dokar kasa, kuma yunkuri ne na murkushe ‘yan Arewa.

Channels TV ta rahoto Abdul-Azeez Suleiman a wajen taron manema labarai yana cewa an kawo wannan batu ne da nufin a hana Arewa takara a zaben 2023.

Suleiman ya yi kira ga jam’iyyun siyasar kasar nan suyi watsi da maganar karba-karba da kuma kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudancin kasar a 2023.

Read also

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

Gamayyar CNG mai kungiyoyi 60 a karkashinta, tana so duk jam’iyyu suyi koyi da gwamnonin Arewa da suka dauki matsayar cewa karba-karba ya saba doka.

APC tana kamfe
Buhari a Kaduna Hoto: cityvoiceng.com
Source: UGC

Ba za ta sabu ba inji CNG

A cewarsa, mutanen Arewa ba za su yarda da wani shiri na hana su neman kujera a zabe mai zuwa ba.

“Muna ganin sabon yunkurin barazanar da ake yi wa mutanen Arewa a matsayin shirin da zai lalata tsarin damukaradiyya, ya kawo rashin zaman da sunan karba-karba.”
“Saboda haka ba za mu yarda da wannan ba.”
“Bayan CNG ta tuntubi masu ruwa da tsaki, shugabanni, da dattawa, ta tsaida matsaya cewa tana tare da ra’ayin kungiyar gwamnonin Arewa da na dattawan Arewa kamar yadda Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana.”

- Abdulaziz Sulaiman

Read also

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

An rahoto CNG tana cewa ware wa wani yanki mukami ya ci karo da kundin tsarin mulki. CNG tace dole a tafi da Arewa a duk abin da za ayi, musamman a zabe.

Dole matasa su tashi tsaye - Osinbajo

A ranar Litinin, 4 ga watan Oktoba, 2021, aka ji mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fada wa matasa su tashi su nemi mulki da gaske a zaben 2023.

Yemi Osinbajo yana so matasa su shiga siyasa domin a rika samun sababbin jini. Osinbajo ya gargadi masu taso wa da cewa ba a bada mulki hakan nan a sama.

Source: Legit

Online view pixel