Bani da N5k na biyan JAMB, shi yasa na koma tuka 'Taxi', inji budurwa mai shekaru 22

Bani da N5k na biyan JAMB, shi yasa na koma tuka 'Taxi', inji budurwa mai shekaru 22

  • Bidiyon wata budurwa mai sana'ar tukin tasi ya girgiza jama'a da yawa lokacin da take ba da labarinta
  • Ta bayyana cewa, rashin kudin biyan JAMB ne ya sa ta fara sana'ar tuka mota don lura da kanta
  • Ta bayyana cewa, ta yi karatun Diploma, amma daga nan ta aje karatu saboda rashin kudin biya

Wata budurwa mai shekaru 22, Lucia Osamo, ta bayyana cewa ta zama direban tasi ne saboda ta kasa samun N5,000 da za ta biya don yin rijistar JAMB.

A cikin wata hira ta musamman da Temitope Wuraola ta Legit TV, ta ce wani lokacin wasu abokan cinikinta maza sukan tsokane ta inda suke cewa ita kyakkyawa ce aikin tasi bai dace da ita ba.

Budurwar ta ce bayan ta kammala Diploma a fannin albarkatun ma'adinai da man fetur daga Auchi Poly, ta zama direbar tasi lokacin da ta lura ci gaba da karatunta babbar matsala ce.

Kara karanta wannan

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

Lucia 'yar shekara ashirin da biyu ta ce dole ne ta dauki nauyin kanta ta fannin makaranta. Cikin fuskar tausayi, ta ce ba za ta ci gaba da karatun jami'a ba saboda ba za ta iya samun kudin jarrabawar shiga jami'a ba.

Bani da N5k na biyan JAMB, shi yasa na koma tuka 'Taxi', inji budurwa mai shekaru 22
Budurwa mai tukin tasi | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Ta ce burinta na yarinta shine ta zama injiniya. Lucia ta ce yawancin mutane ko yaushe suna yin sharhi kan yadda kankanta yake. Lucia ta ce wasu mutane suna fasa tafiya a motarta saboda ita mace ce.

Kalli bidiyon hirar:

Martanin jama'a

Jama'a da dama a kafafen sada zumunta sun yi martani kan labarin wannan budurwa.

Bishop Tonia Ugochukwu ya ce:

"Abin bakin ciki ne ga zamanin da za su dauki nauyin BBN inda za su dauki nauyin jefa kuri'a kan mata ke nuna tsiraicinsu da nonon roba amma ba za su iya taimaka wa ko tallafa wa matan da ke yin kasuwancin halal ko fafutuka ba. Ina kuka ga wannan zamani!"

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

Peace Udoh ya ce:

"Allah shine ƙarfin ki 'yar uwa, zai juya lamurranki ga alheri. Ki yi imani da shi don labarin ki zai canza nan ba da dadewa ba."

Adams Zamani Abdulmalik Inyass yace:

"Allah zai dubi lamarinki 'yar uwata. Kasar nan sam bata murmushi."

Saviola Sylva Lahadi ya ce:

"Ko yaushe ku yi imani da kanki kuma ki dogara ga Allah gaba daya, ba ya yin bacci ko runtsawa. Kin yi kokari."

Ya kamata 'yan Najeriya su yabawa Buhari bisa daina layin sayen man fetur, MURIC

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai (MURIC) ta ce rikicin man fetur da ke gudana a Burtaniya wata dama ce ga 'yan Najeriya su yabawa Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa, daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce a karkashin mulkin Buhari, Najeriya ta yi sallama da layin sayen man fetur.

A cewarsa:

“Burtaniya ta fada cikin karancin mai wanda ya haifar da dogayen layuka a gidajen mai a cikin makwanni biyu da suka gabata. Daga cikin gidajen mai 8,000 a Burttaniya, kusan kashi biyu bisa uku na gidajen mai 5,500 sun kare.

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel