Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

  • 'Yan kasuwan kasar Ghana sun koma cin zarafin 'yan kasuwan Najeriya mazauna kasar a cikin watan Satumban da ya gabata
  • An gano cewa, kungiyar 'yan kasuwan kasar sun rufe daruruwan shagunan 'yan kasuwan Najeriya
  • Kungiyar habaka kasuwancin kasar ta bukaci harajin $1 million (N410m) daga 'yan kasuwan idan suna son a bude musu shaguna

Ghana - Watanni goma bayan jerin sasanci da aka yi tsakanin gwamnatin Najeriya da hukumomin Ghana wanda aka yi shi domin shawo kan matsalar rikicin da ya kawo rufe shagunan 'yan kasuwan Najeriya a Ghana, lamarin ya sake barkewa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

'Yan Najeriya masu tarin yawa sun rasa hanyar neman abincinsu saboda rikicin da ya sake barkewa duk da kiran gwamnatin tarayya da aka yi domin ta kai musu dauki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya
Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa, tsakanin ranakun ashirin zuwa da hudu na watan Satumba, 'yan kungiyar 'yan kasuwan Ghana, sun rufe wasu shagunan 'yan Najeriya a cikin zanga-zangarsu ta dakile bakin haure daga kasuwanci a kasar.

A yayin sakewar barkewar rikicin, 'yan kasuwa da ke Sabuwar Juaben da ke kudancin birnin aka tunkara.

Masu kai farmakin sun ce dokokin Ghana ba su bada damar da bakin haure za su shiga kasuwancin kasar haka ba.

An rufe shaguna masu tarin yawa, kari kan shaguna dari biyu da hamsin da aka rufe a watan Disamban 2019, Yulin 2020 da Disamban 2020.

Da yawa daga cikin 'yan kasuwan sun rasa inda za su yi kuma suna ta rokon jama'a abinci. Amma kuma sun kasa dawowa gida duk da da,ar da gwamnatin tarayya ta basu na dawowa gida.

Kara karanta wannan

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Sun ce babu wani abinda zai rike su a gida Najeriya idan sun dawo. Ana tsaka da rikicin, kasar Ghana ta kallafa wa 'yan kasuwan Najeriya da bakin haure harajin naira miliyan dari hudu da goma wacce za su bai wa Ghana Investment Promotion Centre (GIPC) kafin a bude musu shagunansu.

Wasu daga cikin 'yan kasuwan sun ce wannan harajin ya fi karfin jarinsu gaba daya da suka mallaka inda suka kwatanta hakan da kokarin gwamnatin Ghana wurin fatattakarsu.

Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, Dave Umahi, ya ce sun gano cewa an kaddamar da yaki kan yankinsu a yayin da ya ke martani kan kashe-kashen da 'yan bindiga ke wa jama'arsu.

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, Gwamna Umahi ya nuna damuwarsa da alhini kan kisan rayuka 12 da aka yi a yankin a makon da ya gabata kuma ya ce babu gaira balle dalili.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar tsaro na jihar a ofishin sabon gwamnan Abakaliki. Ya zargi wasu Ndigbo da ke zama a kasashen ketare da shirya rigingimun tare da daukar nauyinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel