'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

  • Miyagun 'yan fashin daji sun halaka wani ma'aikacin jinya na jin kai mai aiki da Medicine San Frontiers (MSF) a Zamfara
  • A yammacin ranar Asabar ne miyagun suka bude wa motar haya wuta inda suka sheke rayuka 3 tare da raunata wani mutum 1
  • Motar na kan hanyar zuwa Shinkafi ne a kan babban titin Shinkafi zuwa Kauran Namoda a jihar Zamfara

Zamfara - A yammacin ranar Asabar, 'yan bindiga sun halaka rayuka mutum uku da suka hada da ma'aikacin jin kai da ke aiki da Medicine San Frontiers (MSF), wanda ke motar haya kan hanyarsa ta zuwa jihar Zamfara.

Ma'aikacin jinyar MSF, Hassan Muhammad, ya na kan hanyarsa ta komawa wurin aiki a garin Shinkafi yayin da 'yan bindigan suka bude wa motarsu wuta kan babban titin Shinkafi zuwa Kauran Namoda, Premium Times.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisar dattawa na barazanar bada umarnin damko Marwa da Monguno

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara
'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sauran mutum biyun da aka kashe su ne Dahiru Scamper da kuma direban motar hayan, Musa Moriki. Akwai wani Shuaibu Buti wanda ya samu miyagun raunika amma ya na babban asibitin Moriki inda ya ke samun kulawar likitoci.

Wata majiya daga iyalan ma'aikacin jinyar da suka bukaci a boye sunansu, sun sanar da Premium Times cewa an mika gawar ma'ikacin jinyar zuwa babban asibitin tarayya da ke Gusau.

"Amma mun samu karfin guiwar zuwa mu dauke shi. Yanzu haka muna Gusau da wasu daga cikin 'yan uwanmu," majiyar danginsa ta ce.

Usamah Abubakar, abokin ma'aikacin jinyan da aka kashe, ya tabbatar da yadda Muhammad ya rasu.

"Hassan ya yi rayuwa cike da bautawa al'umma da Ubangijinsa tare da ceton rayuka. A abinda na sani game da shi, mutum ne mai kankan da kai, natsuwa da kuma rikon amana," Abubakar yace.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

Har a lokacin rubuta wannan rahoton, ba a samu kakakin rundunar 'yan sandan jihar ba, Sanusi Abubakar domin tsokaci.

2023: Ta yuwu Najeriya ta samu 'yan takara 2 marasa amfani idan aka dubi yanki, Sanusi

A wani labari na daban, Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya ce alanta mulkin shugaban kasa ga yanki zai iya sa kasar nan ta kare da 'yan takara biyu marasa amfani a 2023.

A yayin jawabi a Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce sau da yawa ya na kushe duk wata tattaunawa da za a yi kan yankin da ya dace ya samar da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.

Manyan jam'iyyu biyu na kasar nan na APC da PDP suna ta cece-kuce kan yankin da zai samar da shugaban kasa. Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce Najeriya ta na bukatar shugaban kasa wanda zai iya amfanar ta ba tare da duban yankinsa ba, TheCable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel